Ahlul BaitiTun al'ummar musulmi tana jaririya a hannun Manzon Shiriya, Muhammadu (s.a.w.a), abokan gaban musulmi daga masu bautar gumaka da yahudawa da nasara da munafukai da masu neman fadanci domin arzurta kansu, suke kokarin kekketa al'ummar da hura wutar sabani da rarraba. Hakika da'awar Musulunci a karkashin jagorancin Manzon Allah (s.a.w.a.) ta fuskanci wannan kaidin ta kuma yi nasara kan yahudawa da mushrikai da munafukai, albarkacin jagoranci Annabi (s.a.w.a) da kuma lizimtar sahabbansa, zababbu. Tarihin yadda Musulunci ya sha kokawa da wadan-nan magabta a zamanin Annabi (s.a.w.a) yana cike da abubuwa masu bayyana mana yadda masu jayayya da Musulunci, magabtan al'umma suka yi aiki da makamin rarrabawa da shuka sabani. Duk wanda ya bibiyi Alkur'ani Mai Girma da Sunnar Annabi (s.a.w.a) da dalilan saukar ayoyin Alkur'anin, sannan kuma ya dubi tarihin farkon sakon Musulunci zai lura da cewa sakon ya yaki wannan ciwon mai neman rusa addini, yakin da ba kakkautawa. Ya kuma gargadi musulmi kan kada su fada cikin sabani da rarraba kamar yadda al'ummar da suka shude suka fada. Alkur'ani ya hori musulmi da hadin kai da riko da juna, ya kuma yi gargadi kan rarraba da sassabawa da jayayya, yana mai suranta irin makomar masu yin hakan da cewa: "...Kuma kada ku yi jayayya har ku raunana, karfinku kuma ya tafi...". Hakika Alkur'ani ya yi gargadi kan jayayya da sabani wanda shi yake kai mutane da makoma mai muni da rauni da ragwanci da kasawa da gushewar karfi da daula. Haka nan kuma ya gargade mu kan zamowa kungiyoyi masu gaba da neman halaka juna, sashi na dukan sashi, sashi na la'antar wani sashin tamkar yadda mushirikai da batattun al'ummai masu keta kalmar Allah da wasa da shari'o'inSa suka kasance. Alkur'ani mai girma yana fuskantar da wannan al'umma da ta hada kai bisa kalmar tauhidi: "...Saboda haka ka tsayar da fuskarka ga addini... wannan shi ne addini madaidaici". Da kuma kira zuwa ga riko da igiyar Allah: "Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba...". Da kuma cewa wannan al'umma guda ce: "Kuma lalle ne wannan al'ummar ku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku biNi da takawa".
|