Ahlul BaitiAbin nufi da 'ya'yansa a wannan aya su ne Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda maganganun malaman tafsiri da ma'abuta tarihi suka sanar da mu. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya karfafa wannan ma'anar wa al'ummarsa sau da yawa, bari mu ambaci kadan daga cikinsu. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Allah Ya sanya zuriyar kowane Annabi daga tsatsonsa, (ni kuma) Ya sanya zuriyata cikin tsatson wannan", yana nufin Aliyu (a.s.) ([57]). Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana rungumar Hasan da Husaini (a.s.), yana cewa: "Dukkan 'ya'yan wani uba dangantakarsu ta ubansu ce, ban da 'ya'yan Fadima, ni ne ubansu, da ni ake dangantasu". Imam Ahmad ya fito da wannan hadisin cikin al-Manakib([58]). Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) yana karfafa matsa-yin Ahlulbaiti (a.s) a kowani muhimmin lokaci, domin al'umma ta koma gare su, ta lizimci tafarkinsu, ta kuma yi riko da soyayyarsu. A ruwayoyi da dama, muna samun cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya nuna mana su a matsayin tudun tsira ga wannan al'umma, yana gwama su da Alkur'ani, yana kuma sanya rawar da za su taka a fagen akida da rike sakon Musulunci, mai lizimtar Littafin Allah ne, ba sa rabuwa da shi. Hakan kuwa don al'umma ta fuskanto su wajen fahimtar Alkur'ani mai girma, da ciro ma'anoninsa da hukumce-hukumcensa. Littattafan hadisi da tarihi sun taru bisa kawo hadisin Annabi (s.a.w.a) da ake kira da Hadisin Nauyaya Biyu (Hadith al-Thakalain). Musulmi sun ruwaito wannan hadisi duk da bambance-bambancen mazhabobinsu na siyasa da fikihu. Za mu ambace shi a nan tare da sashin isnadinsa (maruwaitan da suka ruwaito shi), kamar yadda masu ruwaya da malaman hadisi suka nakalto. 1- Hadisus Sakalain (Nauyaya Biyu): Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
"Na kusata da a kira ni in kuma amsa, amma ni mai bari muku abubuwa masu nauyi guda biyu ne, su ne kuwa: Littafin Allah Mai girma da Daukaka, da kuma zuriyata. Littafin Allah wata igiya ce da aka sako ta daga sama zuwa kasa, zuriyata kuwa su ne mutanen gidana (Ahlulbaiti). Allah Mai tausasawa Ya ba ni labari cewa su biyun ba za su taba rabuwa ba har abada har sai sun iske ni a bakin tafki. To ku lura da yadda za ku rike su a bayana([59])". Al-Shibrawi al-Shafi'i ya nakalto cikin littafinsa mai suna al-Ithafu bi hubbil Ashraf, cewa:
|