Ahlul Baiti"Allahu Akbar! Bisa kammalar addini da cikar ni'ima da yardar Ubangiji da Manzancina da walittakan Aliyu([46])". Akwai ayoyi masu yawa, wadanda wannan karamin littafi ba zai iya tattaro su ba, da suke magana a kan matsayin Ahlulbaiti (a.s) da karamar su da girman mutanen ciki, wadanda wasu daga cikinsu sun kebanta ne ga Uban wannan itace mai tsarki, wato Imam Ali (a.s.). Mai karatu zai iya samun wadannan ayoyi cikin littattafan tafsiri, hadisi, tarihi da kuma masu bayani kan falalolin wadannan taurari da kuma wadanda suka yi magana kan Asbabun Nuzul na wadannan ayoyi. To amma bari mu kawo kadan daga cikin irin wadannan ayoyi, su ne kuwa: (1). Fadin Allah Madaukakin Sarki: )إنَّمَا أنْتَ Ù…ÙنْذÙرٌ ولÙÙƒÙلّ٠قَوْم٠هَادÙ) "Abin sani kawai kai mai gargadi ne kuma a cikin kowadanne mutane akwai mai shiryarwa". (Surar Ra'ad, 13:7) Hadisi ya zo cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sanya hannunsa bisa kirjinsa, ya ce: "Ni mai gargadi ne, ko wadanne mutane kuma suna da mai shiryarwa", sai ya yi nuni da hannunsa zuwa Ali (a.s.), sai ya ce kai ne mai shiriyarwan, Ya Aliyu, da kai masu shiryuwa za su shiryu a bayana([47])". (2). Fadar Allah Madaukakin Sarki:
Ø£Ùَمَنْ كَانَ Ù…ÙؤمÙنًا كَمَنْ كَانَ ÙَاسÙقًا لا يَسْتَوÙونَ "Shin wanda ya zama mumini yana kamar wanda ya zama fasiki? Ba za su yi daidai ba". (Surar Sajada, 36: 18)
|