Ahlul Baiti"...amma wallahi - sai ya mika hannunsa zuwa kirjinsa - akwai makamin Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da mu, takobinsa da sulkensa, kuma wallahi, muna da Mus'hafin Fadima tare da mu, babu wata ayar Littafin Allah a cikinsa, shi dai shifta ce daga shiftar Manzon Allah (s.a.w.a.) Aliyu kuwa shi ne ya rubuta shi da hannunsa([95])". Hakika wasu sun shiga wahami kan cewa Imam Sadik (a.s.) - wal iyazu billahi - yana ba da labarin samuwar wani Alkur'ani ne ban da wannan Alkur'anin da ke hannunmu, sai wadansu suka dauki wannan waha-mi a matsayin wata hujjar shuka barna tsakanin mutane. Idan muka koma ga kalma Mus'haf cikin harshen larabci zai sa mu fahimci ma'anar wannan magana ta Imam (a.s.). Ragib al-Isfahani yana cewa: "Sahifa ita ce duk wani abu shimfidadde, kamar shimfidar kunci, ganye ko wani shafi da ake rubutu a kansa, jam'inta kuwa shi ne Saha'if ko kuma Suhuf. Allah Ta'ala Yana cewa: "Suhufin Ibrahima da Musa", "Suna karanta Suhufai tsarkakakku, cikinsu akwai litattafai masu kima". An ce abin da ake nufi da Suhufan shi ne Alkur'ani, sai Ya sanya su takardu da litattafai a cikinsa domin tara wani abu bayan abin da yake cikin sauran littattafan Allah. Shi kuwa Mus'hafi shi ne abin da aka yi shi mai tattara takardu rubutattu, jam'insa kuwa shi ne Masahif([96])). Saboda haka kalmar Mus'haf, a ma'anonin da muke amfani da su a yau, tana nufin littafi ba suna ne wanda ya kebanta da Littafin Allah (Alkur'ani) ba. Shi suna ne na kowane littafi da ya tattara takardu ko fatu (kamar yadda ake rubutu a jikin fata a zamanin da). Ana kiran Alkur'ani da sunan Mus'haf ne domin shi mai tattare ne da takardu. Alkur'ani mai girma yana da sunaye daban-daban kamar haka: Alkur'ani, al-Zikr, al-Furkan da kuma al-Kitab([97]), wahayi dai bai kira shi (Alkur'ani) da sunan Mus'haf ba, kai dai musulmi su suka ba shi wannan suna yayin da suka tara shi, don bayan tarawan ya zamanto wani tari ne na takardu (suhuf).
|