Ahlul BaitiTo haka ne tafarkin Ahlulbaiti (a.s) yake fayyace manufar shiriya da bata da kuma cewa Allah (S.W.T.) bai halicci mutane suna batattu ko shiryayyu ba. Sai dai Ya bar musu zabi, Ya ba su nufi, Ya kuma bayyana musu hanyar alheri tare da gargadi kan hanyar sharri da halaka, Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle ne Mu, Mun shiryar da shi (mutum) ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai kafirci". (Surar Insan, 76: 3) Kuma Yana cewa: "Kuma Muka shiryar da shi ga hanyoyi biyu". (Surar Balad, 90: 10) Watau Mun sanar da shi hanyar alheri da ta sharri, zabi kuma na gare shi. Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fassara ayar da cewa: "Su dai hanyoyi ne guda biyu, hanyar alheri da hanyar sharri. Kada hanyar sharri ta fi soyuwa gare ku bisa hanyar alheri([187])". Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) ya zabi ra'ayi tsarkakakke na bayani kan halayyar dan'Adam na alheri ko sharri, da wata ka'ida: "Babu Jabru ba tafwidhu, sai dai al'amari ne tsakanin al'amurra biyu, watau mataki tsakanin matakai biyu". Yayin da aka tambayi daya daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s), shin akwai wani mataki tsakanin tilasta-wa (jabru) da sajarwa (tafwidh)? Sai ya amsa da cewa:
|