Ahlul Baiti(Muhammad Muhammad Fahham) In an duba za a ga cewa hanyar hada kan al'umma bude take ga duk mai ikhlasi daga 'yan'uwa musulmi, wajibi ne su hada sahu guda, su jefar da sassabawa da 'yan garanci, su tuge dalilan rarraba, su gurfanar da ra'ayoyin ilmi gaban bincike da tattaunawa domin a gano gaskiya. Mu muna kiran al'ummar musulmi ko ina suke da su fahimci irin halin kunci da musulmi suke ciki na siyasa da zamantakewar jama'a, su kuma yi aiki kan hada kan musulmi da watsar da rarrabuwa, kuma su gano wanda yake rura wutar sabani da 'yan garanci, domin su nesance shi. Domin ya wajaba mu sani cewa muna fama da kulle-kullen Yahudawa Sahyoniya da 'yan mulkin mallaka na Gabashi da Yammaci da 'yan barandansu. Daga karshe, muna rokon Allah Mai Daukaka, Mai iko da Ya hada kan al'ummar musulmi, Ya nisantar da masu dasisa da masu rura wutar fitina tsakanin al'ummar musulmi da tozarta masu aikin tabbatar da shari'ar Allah da masu kira zuwa gare Shi. Domin akwai taimakawa abokan gaban Allah da hidima ga azzaluman duniya cikin raunana hadin kan musulmi da yada rarraba tsakanin rundunonin masu jihadi da kira zuwa ga Allah. "Kuma ka ce: "Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9: 105). Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Wallafar: Mu'assasar Al-Balagh Fassarar: Ammar Kumo |
back | 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 | next |