Ahlul BaitiYa kuma sake cewa: "Shi Alkur'ani ya kasance a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a.) a tare yake a wallafe kamar yadda yake a yau. Ya kafa hujja da cewa Alkur'ani ya kasance ana darasinsa ana kuma haddace shi a wancan zamani har aka ayyana wata jama'a cikin sahabbai da cewa sun haddace shi, da kuma cewa ana bijiro da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) ana karanta masa, sannan kuma wata jama'a daga cikin sahabbai kamar su Abdullahi bn Mas'ud da Ubayyu bn Ka'ab da sauransu, sun sauke Alkur'ani gaba ga Annabi (s.a.w.a) sau da yawa. Duk wannan yana nunawa cewa shi Alkur'ani ya kasance tararre ne jerarre, ba yankakke ba, ba kuma a watse yake ba. Ana riskar wannan hakika kuwa ba tare da bukatar wani dogon tunani ba. Sayyid Murtadha ya ci gaba da cewa wanda ya saba wa wannan ra'ayi daga cikin Imamiyya da Hashawiyya, to ba a dogaro da wannan sabawa ta su domin sabawa da wannan ra'ayi abin dangantawa ne ga wasu mutane daga cikin ma'abuta hadisi wadanda suka nakalto hadisai masu rauni, amma suna zaton ingantattu ne. Kuma ba a barin abin da aka tabbatar da ingancinsa domin irin wadannan raunanan hadisai([89])". Sannan kuma sai ya ce:"Abin da ya shahara a wajen malaman Shi'a da masu bincikensu, kai ba ma kawai shahara ba har ma babu jayayya a cikinsa, shi ne rashin ragi ko kari cikin Alkur'ani([90])". Shaihin malaman hadisi Muhammad bn Ali bn Husain bn Babawaihi al-Kummi, wanda ake wa lakabi da "Saduk" (ya rasu a shekara ta 381), kuma mawallafin littafin Man La Yahdhuruhul Fakih da kuma dimbin muhimmman littattafai, ya fada cikin littafinsa mai suna I'itikadatul Saduk cewa: "Akidarmu game da Alkur'ani mai girma wanda Allah Ya saukar wa AnnabinSa Muhammadu (s.a.w.a) shi ne abin da yake cikin bangwayen nan biyu, shi ne wanda yake hannun mutane bai wuce wannan ba - har ya zuwa inda yake cewa - kuma duk wanda ya danganta gare mu cewa muna fadin wai Alkur'ani ya fi haka to shi makaryaci ne". Sannan ya shiga kawo hujjoji kan hakan, mai son karin bayani yana iya duba cikamakin maganan tasa([91]). Shugaban jama'ar Shi'a, Abu Ja'afar Muhammad bn Husain al-Dusi (wanda ya rasu a shekara ta 460 hijiriyya), mawallafin littafin Al-Khilaf da Al-Mabsud da Al-Tahzib da Al-Istibsar da sauransu, ya fada cikin littafinsa na tafsiri mai suna Al-Tibyan cewa([92]): "Amma zancen kari (cikin Alkur'ani) da tawaya, suna daga cikin abubuwan da su ma ba su dacewa da shi domin kari cikinsa, abu ne wanda aka yi ijima'i kan batacce ne. Tawaya kuwa, bisa zahirin ra'ayin musulmi, babu shi, hakan kuwa shi yafi dacewa da abin da ya inganta a mazhabarmu, shi ne kuwa abin da Al-Murtadha ya goyawa baya, shi ne kuma zahirin ruwayoyi, - har zuwa inda yake cewa - ruwayoyinmu kuma suna karfafa juna kan kwadaitar da karanta shi da riko da abin da yake ciki, da dawowa da duk wata sassabawar hadisai masu magana kan rassa (furu'a) zuwa ga Alkur'ani. Hakika an ruwaito wani hadisi da ba wanda yake musa shi, daga Annabi (s.a.w.a) cewa, Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Ni mai barin Nauyayan Abubuwa guda Biyu ne tare da ku, wadanda idan kuka yi riko da su ba za ku bata a baya na ba: (su ne) Littafin Allah da Zuriyata, Ahlulbaiti, don ba za su rabu da juna ba har sai sun riske ni a bakin tafki". Wannan yana nuni da cewa shi Alkur'ani samamme ne a dukkan zamani, domin ba zai yiwu ya yi umurni da riko da abin da ba za mu iya riko da shi ba, kamar yadda Ahlulbaiti (a.s) da wanda bin fadarsa yake wajibi samammu ne a duk lokaci. To idan wanda yake tare da mu an hadu a kan ingancinsa to ya kamata mu shagaltu da tafsirinsa da bayyana ma'anoninsa, mu bar komawa bayan wannan). Allama Shaikh Muhammad Jawad al-Balagi ya tabbatar da wannan hakika cikin tafsirinsa Ala'ur Rahaman fi Tafsiril Kur'an, wato dawwamar Alkur'ani da kubutarsa daga jirkita da gurbata, inda yace:
|