Ahlul BaitiDon haka ne ita Sunna mabubbuga ce wacce ba ta kafewa, kuma gaskiya ce wacce barna bata taho mata a bayanta ko a gabanta. Sunna ita ce amintacciya mai ayyana dokokin rayuwa da kuma tsarin jin dadin dan'Adam, kuma ita madawwamiya ce dawwama irin ta Alkur'ani mai girma. Allah Ta'ala Ya ce: وما آتَاكÙم٠الرَّسول٠ÙÙŽØ®ÙØ°Ùوه٠وَما نَهاكÙمْ عَنْه٠ÙَانْتَهÙوا" Abin da Manzo ya zo muku da shi, ku karba, abin da kuma ya hane ku, to ku hanu...". (Surar Hashr, 59: 7) لَقَدْ كَانَ Ù„ÙŽÙƒÙمْ ÙÙÙŠ رَسÙول٠الله٠أÙسْوَةٌ Øَسَنَةٌ Ù„Ùمَنْ كَانَ يَرجÙÙˆ اللهَ وَاليَومَ الآخÙر "Hakika abin koyi mai kyau ya kasance muku daga Manzon Allah, da duk wanda yake kaunar Allah da kuma ranar lahira...". (Surar Ahzab, 33: 21) Ùإنْ تَنَازَعْتÙمْ ÙÙÙŠ شَيْء٠ÙَرÙدّÙوه٠الى الله٠وَالرَّسÙول٠"Idan kuka yi jayayya a wani abu to ku mai da (hukumcinsa) ga Allah da Manzo...". (Surar Nisa'i, 4:59) Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) da wadanda suka dauki tafarkinsu wajen tafsiri da hadisi da fikhu da shari'a da akida, sun lizimci wannan hanyar, sun kuma yi gwagwarmaya, sadaukarwa, daurewa cutarwa, shiga kurkuku, kisa, azabtarwa da kuma kora duk a dalilin kare sunna mai tsarki da kira zuwa ga dacewarta da Littafin Allah mai girma. Hakika an bijirar da Sunna tsarkakakkiya ga coge da karkatarwa da jirkitarwa wanda masu yi wa Musulunci dasisa, karya da kiyayya suke yi domin muzanta wannan dawwamammen sako na Ubangiji, domin kuma su karkatar da tafarkin al'ummar Musulunci. Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna fagen kan gaba wajen kiyaye Sunna tsarkakakkiya da daukar ta da kuma isar da ita da gaskiya da amana, da kuma bayyana abubuwan da ta tattara na bayani mai zurfi.
|