Ahlul BaitiAbin da ya faru har ya sa aka saukar da wadannan ayoyi dominsa yana nuni ne da matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kaiwarsu matuka wajen aikatawa da lizimtar shari'a da kuma fuskantar Allah cikakkiya. Kuma su ne mutanen kirkin da aka yi musu albishir da aljanna, to duk wanda ya yi koyi da su, ya yi tafiya a kan tafarkinsu, to za a tashe shi tare da su. Zamakhshari ya kawo bayani kan wannan aya cikin tafsirinsa. Ga abin da ya ce: (Daga Ibn Abbas (r.a.): Wata rana Hasan da Husaini (a.s.) sun yi rashin lafiya, sai Manzon Allah (s.a.w.a.) tare da wasu mutane suka ziyarce su don gai da su, sai ya ce wa Imam Ali (a.s.): Ya Abal Hasan, da dai ka yi bakance kan rashin lafiyar 'ya'yanka. Sai Aliyu da Fadima da baiwarsu Fiddha suka ce idan suka sami sauki daga wannan ciwo nasu, za su yi azumin kwanaki uku. Sai kuwa suka warke, alhalin kuwa a wannan gida mai albarka babu wani abu na daga abinci. Sai Aliyu (a.s.) ya yi bashin sa'i uku na Sha'ir daga wani Bayahude mai suna Sham'un Alkhaibari, daga nan sai Fadima ta nika sa'i guda ta yi gurasa biyar, adadin mutanen gidan. Sai ta sanya gurasar a gabansu domin su yi buda baki, bayan lokacin shan ruwa ya yi. Sun shirya za su ci kenan sai ga wani almajiri ya tsaya a kofa ya ce: Assalamu Alaikum, mutanen gidan Muhammadu (s.a.w.a), ni miskini ne daga miskinan musulmi, ku ciyar da ni, Allah Ya ciyar da ku daga abincin aljanna. Sai suka fifita shi (wajen cin abincin) wato suka dauka suka ba shi, su kuwa suka kwana ba su dandani kome ba, sai ruwa, sannan kuma suka wayi gari da azumi a bakinsu. Da suka kai maraice, suka sake shirya abincin buda baki, sai ga wani maraya ya tsaya a kofa ya yi bara, nan take suka dauki abincin suka ba shi, suka kwana haka. A rana ta uku ma suka ci gaba da azumi, shi ma da lokacin buda baki ya yi suka shirya dan abin da ya sawwaka, a nan ma sai ga wani kamamme ya zo shi ma yana neman abin da zai ci. Sai suka dauki abin da suka tanada suka ba shi. Da suka wayi gari sai Aliyu (r.a.) ya kama hannun Hasan da Husaini suka nufi gurin Manzon Allah (s.a.w.a.). Yayin da Annabi (s.a.w.a) ya gansu suna karkarwa kamar 'ya'yan tsaki saboda tsananin yunwa, sai ya ce: "Babu abin da zai bakanta mini rai fiye da halin da na ganku a ciki". Sai ya tashi ya tafi tare da su sai ya ga Fadima (a.s.) tana wurin sallarta alhali bayanta ya mannu da cikinta, idanunta sun fada. Ganinta cikin irin wannan hali ya bakanta wa Manzon Allah (s.a.w.a.) rai, sai ga Jibrilu (a.s.) ya sauko ya ce: "Karbi ya Muhammadu, Allah Na tayaka murna batun Ahlulbaitinka", sai ya karanta masa wannan surar([24]). Ta Shida:
Hakika ayoyin Alkur'ani masu yawa sun sauka da batun Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s.) wanda aka yi tarbiyyarsa cikin gidan Manzon Allah (s.a.w.a.) tun yana karami([25]). Ya tashi karkashin kiyayewarsa (s.a.w.a) don haka ya kwaikwayi halayensa. Ya yi imani da shi, gaskanta shi da kuma binsa tun yana dan shekara goma. Sannan kuma Imam Ali (a.s.) ya kasance mai daukar tutar Manzon Allah (s.a.w.a.) kuma shi ne jarumin sojansa wanda ya kere kowa a dukkan yake-yakensa, da suka hada da Badar, Uhud, Hunain, Ahzab, Khaibar, Zatu Silasil da dai sauransu. A saboda irin jaruntar da ya nuna a irin wadannan yakuna, ya sa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kansa ya jinjina masa da bayyanar da wasu kalmomi dawwamammu da suka kasance ado ga littatta-fan tarihi sannan kuma abin koyi na koli cikin sadaukar-wa da kuma jihadi.
Idan muka yi bincike kan asbabun Nuzul (dalilan saukar ayoyi), za mu samu cewa abin da ya sauka dangane da Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib (a.s.) - ban da abin da muka ambata na Ahlulbaiti (a.s) - suna bayani ne: 1. Kan jaruntar Aliyu (a.s.) gwarzontaka da kuma sadaukarwarsa a kan tafarkin Allah. 2. Kan hakurinsa bisa cutarwa da izgili. 3. Kan gudun duniya, takawa ilimi da kuma kaunarsa ga muminai. Bari mu ambato wasu misalai kamar haka:
|