Ahlul Baiti"Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda daya, kuma Ni Ubangijinku ne, sai ku bauta Mini". Kamar haka ne Alkur'ani ya sanya matakan hada kan al'umma kamar haka: 1. Wanda ake wa bauta Shi kadai ne, kuma abin nema shi ne kadaita Shi da bauta masa. 2. Manufar addini ita ce tsayin daka da kuma muwafaka da halittar da Allah Ya yi mutane a bisa kanta. 3. Cewa wajibi ne kan al'umma ta tara karfinta wurin kira zuwa ga Musulunci da tabbatar da al'umma mai kira zuwa ga alheri da umurni da kyakkyawa da hana mummunan aiki, da daukar sakon Allah (S.W.T.) zuwa ga 'yan'Adam baki daya: "Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri da kuma hani daga abin da ake ki". An umurci musulmi da wannan aikin a madadin rarraba da sabani da jayayya domin kada su halakar da karfinsu kan kokawan cikin gida har ma su raunana su zamo abin hadiyewa ga abokan gaba. Alkur'ani mai girma yana kiran hankulanmu domin mu gane dalilan sabani da kuma tabbatar da tushen hanyoyin warware shi: (a). Sabani kan shari'a da tunani irin na Musulunci wajibi ne a mai da shi ga Alkur'ani da Sunna. "Idan kun yi jayayya cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa...".
|