Ahlul BaitiMuhammad bn Ahmad al-Zahabi ya fadi game da shi cewa: "Musa ya kasance daga masu (gwanayen) hikima kuma daga bayin Allah masu tsoron Allah([148])". Kamaluddin Muhammad bn Dalha al-Shafi'i ya ce: "Shi ne shugaba mai girman alkadari, mai madauka-kin al'amari, babban mujtahidi mai kyautata ijtihadi, wanda ya shahara da ibada, mai dogewa bisa biyayyar Allah, wanda ya shahara da karamomi. Yana kwana yana sujjada da tsayuwa, cikin yini kuwa yana mai sadaka da azumi. Saboda tsananin afuwarsa da kauda kai ga barin masu zaluntarsa aka yi masa lakabi da Kazimu (mai hadiye fushi) ([149])". Mu'umin Shabalanji ya ce: "Musa al-Kazim (r.a.) ya kasance mafi yawan ibada a zamaninsa kuma mafi ilmi([150])". 8- Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.): Amma batun dansa wato Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.) kuwa, to hakika ya kasance tamkar mahaifinsa wajen ilmi da tsantsaini da cikar kyawawan halaye. Ya karbi ragamar shugabancin addini da nauyin Imamanci a bayan babansa. Ya kai matsayi mai daukaka da daraja wanda ya tilastawa halifan Abbasiyawa Ma'amun ya nada shi magajinsa a bayansa, duk da gaba da fito-na-fito da ke tsakanin Alawiyyawa da Abbasiyawa. Hakika malamai sun ba da shaida a majalisun ilmi da muhawara, kan matsayin Imam Ali Ridha wajen ilmi da karimci da siffantuwarsa da tsantsaini da takawa. Ga wasu daga cikin wadannan maganganu:
|