Ahlul Baiti"Lalle ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, wadannan su ne mafifita alherin halitta" (Surar Bayyina, 98:7) Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Ya Aliyu, mafifita alherin halitta (a cikin wannan aya) su ne, kai da 'yan shi'arka([53])". (8). Fadar Allah Madaukakin Sarki cewa:
( أجَعَلْتÙÙ… سÙقايَةَ الØاجّ٠وعÙمَارَةَ المَسْجÙد٠الØَرام٠كَمَنْ آمَنَ بالله٠واليَوم٠الآخÙر) "Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira kuma ya yi jihadi domin Allah?..." (Surar Tauba, 9: 19) Lalle wadannan su ne Abbas da Dalha, wanda ya yi imani kuwa shi ne Aliyu (a.s.). Akwai wasu ayoyi da dama a kan wannan lamari da muke magana a kansa, amma za mu takaita saboda takaitawa. Ahlulbaiti (a.s.) Cikin Sunnar Annabi
Dukkan wanda ya bibiyi sunnar Manzon Allah (s) da tarihinsa na aikace da kuma alakarsa da mutanen gidansa wadanda nassin Alkur'ani ya kawo, sannan shi (Manzo) kuma ayyanasu (Aliyu da Fadima da 'ya'yansu biyu), zai san cewa mutanen wannan gida suna da wata rawar da za su taka a bangaren nauyin rike sako da kuma wayewar wannan al'umma. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance mai tsare-tsare domin al'ummar tasa da kuma shirya da ita domin ta karbi wannan ni'ima ta Ahlulbaiti (a.s), da umarnin Allah (S.W.T.). Hakika wannan yanki mai haske na tsare-tsaren Annabi (s.a.w.a), wadanda ya yi da umurnin Allah, ya soma ne da aurar da Fadima (a.s.) ga Imam Ali (a.s.), da dasa wannan itaciya mai albarka, domin rassanta su mamaye sansanin wannan al'umma, tsawon rayuwarta. An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) yayin da ya aurar masa da Fadima (a.s.) cewa: "Lalle Allah Madaukakin Sarki Ya umurce ni da in aurar maka da Fadima bisa sadaki gwargwadon nauyin miskalin azurfa dari hudu, shin ka yarda da hakan". Sai Aliyu (a.s.) ya ce: "Lalle na yarda da hakan, Ya Manzon Allah". Anas bin Malik ya ce: Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Allah Ya hada kanku, Ya arzurta kokarinku, Ya albakace ku, Ya kuma fitar da zuriya mai albarka". Sai Anas ya ce: "Wallahi, hakika kuwa Allah Ya fitar da zuriya mai albarka daga gare su"([54]).
|