Ahlul BaitiManzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Adalci na sa'a guda ya fi ibadar shekaru saba'in na sallar dararensu da azumtar yininsu. Zalunci a hukumci na sa'a guda kuma ya fi tsanani da girma wajen Allah a kan sabon shekara sittin ([220])". Jabir bn Abdullah al-Ansari (r.a.) ya ce: 'Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya nemi yardar wani sarki da abin da yake fusata Allah, to ya fita daga addinin Allah ([221])". Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya shugabanci mutum goma sannan bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar lahira hannayensa da kafafunsa da kansa na cikin ramin gatari ([222])". Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk mutumin da ya shugabanci wani al'amari na musulmi, sannan ya rufe kofa (ya ki sauraronsu) to yana cikin azabar Allah Mai Girma da Daukaka da la'anarSa har sai ya bude kofarsa ga mai wata bukata da mai (karar) wani zalunci, sun shigo ([223])". Kamar haka A'imma (a.s.) suke tarbiyyar mabiyansu da karkato da ra'ayin jama'a zuwa ga canji da gyara da shiga fagen siyasa ta hanyarta ta asali. (2). Yankewa daga Azzalumai: Bayan shiryarwa da tarbiyya kan munin zalunci, Ahlulbaiti (a.s) sun kara da umurni da yanke hulda da azzalumai, kamar yadda ya zo cikin hadisi cewa: "Duk wanda ya yi tafiya tare da azzalumai, alhali yana sane da cewa azzaluman ne, to hakika ya fice daga Musulunci" da kuma cewa: "Mai aikata zalunci da mai taimaka masa da mai yarda da shi dukkansu masu tarayya da juna ne". Haka nan suke kira da yanke hulda da azzalumai da rashin taimaka masu. An ruwaito cikin hadisi cewa:
|