Ahlul Baiti



"Kuma kyakkyawan karshe tana tabbata ga masu tsoron Allah". (Surar A'araf, 7: 128)

Jin haka, ya sa Hisham ya tsare shi ([240]).

To a cikin kurkukun ma Imam Bakir (a.s.) bai yi shiru ba, ya wayar da kan fursunoni kan batutuwan siyasa da jihadi har fursunonin suka sami tasirin wa'azinsa, inda suka tayar da hargowa a cikin kurkukun. Ganin haka, sai shugaban kurkukun ya isar da lamarin zuwa ga Hisham, inda shi kuma ya yi umarni da a fitar da Imam (a.s.) daga kurkukun a mai da shi birnin Madina, a hannun wani dan aiken sarki ([241]).

Muhammad bn Jarir Tabari ya rubuta cewa dalilin da ya sa aka mai da Imam Bakir (a.s.) zuwa Madina shi ne bazuwar tasirinsa kan tunanin mutanen Sham sakamakon wata muhawara da ta gudana tsakaninsa da wani shugaban kiristoci([242]).

A wata muhawara da ta gudana tsakanin Hisham bn Abdul Malik da Zaid, a lokacin da labarin yunkurin Zaid din ya isa kunnen Hisham, Hisham ya ce da Zaid:

"Na sami labarin kana ambaton halifanci kuma kana burinsa, alhali kai ba ka cikin mazowansa, kuma kai dan baiwa ne".

Sai Zaid ya mayar masa da martani da cewa, Annabi Isma'il dan baiwa ne kuma Allah Ta'ala Ya ba shi annabta. Sannan Hisham ya dora ambaton Imam (a.s.) da zagi, yana mai tambayan Zaid da cewa:

"Dan'uwanka Bakara kuwa...", sai Zaid ya amsa masa da cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ambace shi da Al-Bakir([243])(*) kai kuma ka kira shi da Bakara (wato saniya), lalle sabaninka da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi yawa kuma za ka saba da shi a ranar lahira kamar yadda ka saba da shi a nan duniya, domin Annabi (s.a.w.a) zai shiga aljanna kai kuwa za ka shiga wuta".

To wannan shi ne matakin da Imam Bakir (a.s.) ya dauka da kuma yunkurinsa na siyasa, har lokacin da ya yi shahada.

To daga nan sai zamanin dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s.), a wannan lokaci na Imam Sadik (a.s.) kuwa bala'i ya yawaita kan al'ummar Annabi (s.a.w.a), ya kuma fi tsanani kan Alayensa (s.a.w.a). Imam Sadik (a.s.) ya kasance shi ne jagoran bijirewa azzalumai ta hanyar siyasa duk da yake bai yi magana bayyananniya kan masu iko ba. Masu yunkuri suna neman shawararsa da goyon bayansa, kai har da neman ya karbi jagorancin harkar, kamar yadda Abu Muslim Khorasani ya bukata yayin da ya mika mubaya'arsa ga Imam. Imam Sadik (a.s.) ya ki karbar wannan mubaya'a saboda rashin cikar sharudda da kasantuwar yanayi bai dace ba, kamar dai yadda ya yi lokacin yunkurin Zaid a zamanin Hisham bn Abdul Malik Ba'umayye.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next