Ahlul BaitiAllah Madaukakin Sarki, Abin nufi da bukata, kamar yadda ya siffanta kanSa cikin wannan Littafi Nasa. Na uku, musulmi sun hadu kan gaskata Annabi (s.a.w.a), suna da Alkibla guda, sun yarda da farillolin Musulunci kamar su salla, zakka, azumi, hajji, jihadi, umurni da mai kyau da kuma hani da mummuna da dai sauransu. Musulmi sun hadu kan haramcin manyan laifuffuka, kamar su zina, shan giya, luwadi, sata, kisan kai, karya, cin rashawa da dai makamantansu. Babu wani sabani tsakanin musulmi cikin ginshikai da tushen imani wadanda suke sanya al'umma ta zama musulma, sun yi ittifaki akan dukkan wadannan gishikai. Saboda haka, wajibi ne a warware mas'alolin ijtihadi da ra'ayoyin ilmi ta hanyar mai da su ga Littafin Allah da tabbatacciyar Sunnar Annabi (s.a.w.a) domin kuwa Annabi (s.a.w.a) ya bar al'ummarsa bisa hanya ma'abu-ciyar haske. Annabi (s.a.w.a) ya ce: "Na bar ku kan hanya mai haske, darenta tamkar yininta. Babu mai karkace mata a bayana sai halakakke". Al'ummar musulmi a yau tana cikin wani matsayi na tarihinta mai bukatar lura da yanayi na ci gaba mai hadari domin tun da dadewa makiya Musulunci suka yi ta kai hare-hare gare su, kama tun daga yakukuwan Salibiyya (wadanda kiristocin Turai suka yi da musulmi), kawo ya zuwa yau din da muke ciki. Su wadannan makiya, kama tun daga su wadannan kiristoci na salibiyya da kuma yahudawan sahyoniya da 'yan korensu, sun fuskanci akidoji da maslahohin musulmi da ruguzawa da kuma makirci, kuma ba su gushe ba tsawon karni na goma sha tara da na ashirin suna babbata wannan al'umma, suna yada rarraba da sabani na siyasa da tunani da bangaranci da jinsi da nahiyanci, ga kuma yakinsu na tunani da kokarin halaka addinin Musulunci. Baya ga haka kuma, ga yada akidojin son duniya kawai da karyata addinai, kamar akidojin jari hujja na Turawan Yamma da gurguzu da dai sauransu. Ga kuma kirkirar jam'iyyu da hukumomi da mahukunta 'yan korensu wadanda suka riki wadannan akidu domin su yaki Musulunci da masu kira da kokarin daukaka shi da shiryar da 'yan'Adam zuwa ga tafarki madaidaici da kuma kubutar da su daga zalunci da bauta wa azzaluman duniya. A waje guda kuma, malaman kwarai suna kiran al'ummar musulmi zuwa ga hadin kai da dawo da martabar musulmi da tabbatar da hukumce-hukumce da tsarin addini, a wani gefen kuwa 'yan koren kafirci, masu sanye da tufafin malamai suna shuka sabani da rarraba da gurbata fuskar Musulunci domin su tabba-tar da hukumcin 'yan koren Turai da sauran makiya Musulunci, masu tsotse arzikin kasashen musulmi da shinfida ikon sahayoniyawa da 'yan jari hujja da 'yan gurguzu. Ya wajaba kan 'yan'uwa musulmi da su kiyaye tare da sanin hakikanin masu yada dafin rarraba da sabani cikin musulmi ta hanyar dasisa da karya da kage-kage ko ta hanyar riko da raunana da kagaggun ruwayoyi da suke cikin littattafan hadisai. Irin wadannan hadisai za a samu cewa malamai da masu bincike sun riga da sun fitar da su daga da'irar ilmi, suna ganin sauya su aka yi. Duk musulmi sun san da hakan kamar yadda Manzon Tsira (s.a.w.a) ya gargadi musulmi a hajjinsa na bankwana da cewa: "Hakika makaryata sun mini yawa kuma za su yawaita. To duk wanda ya yi min karya da gangan ya tanadi mazauninsa a wuta. Idan hadisi ya zo muku, ku gwada shi da Littafin Allah da Sunnata, abin da ya dace da Littafin Allah, to ku rike shi, abin da kuwa ya saba da Littafin Allah da Sunnata, to kada ku yi riko da shi([249])". To idan dukkanmu muna sane da wannan, saboda maslahar waye masu neman rusa addini suke rubuta littattafai da mujallu masu yada rarraba da sabani tsakanin musulmi da kafirta juna da shuka gaba cikin zukata? - domin maslahar wa suke wannan mugun aiki, musamman ma a wannan lokacin mai hadari? Alhali Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:
|