Ahlul BaitiTauhidi A Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) "Farkon addini sanin Allah, cikar saninSa kuwa kadaita Shi, cikar kadaita Shi kuwa tsarkake niyya gare Shi([164])". "Allah ba Ya karbar aiki ba tare da an sanShi ba, babu kuma yadda za a sanShi sai da aiki. To wanda ya sani sanin zai shiryar da shi zuwa aiki, wanda kuwa bai yi aiki ba, to ba sani a gare shi. Ku saurara! Lallai shi imani sashinsa daga sashe yake([165])". Tauhidi ka'ida ce ta Musulunci, shi ne kuma ginshikin fahimta da tunani, kuma shi ne matattarar ilmi da aiki. Shi ne matakin farko da kuma ka'idar sauya shari'a da ka'idoji da halaye kwarai da kuma tafarkin tunani. Manufar Tauhidi tana matsayin ginshiki wajen gina wayewa ta Musulunci wacce ta kebanta da rininta na tauhidi; Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Rinin Allah! Kuma wane ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, masu bautawa ne". (Surar Bakara, 2: 138) Rinin nan na tauhidi wanda ya banbanta wayewa irin ta Musulunci daga wata wacce ba ita ba, kuma wanda shi ya ba ta siffofi iyakantattu na aike (daga Allah) shi ya sanya wa rayuwar musulmi da tunaninsa wani zubi kebantacce. Lallai Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki su ne tushen tunani na matsalolin akida. Hakika sun ba mu bayani cikakke kan akidar tauhidi, sun bayyana mana samuwar Allah Mahalicci, Mai Girma da Daukaka, sun kebance mana bayanin siffofinSa na kamala tare da tabbatar masa da cikakkiyar tsarkaka daga dukkanin nakasa. Ginshikan wannan akidar ta tauhidi sun cika, musulmin farko kuwa sun yi imani da su, kamar yadda suka ji su daga Manzon Allah (s.a.w.a.) suka kuma karanta su cikin Littafin Allah Mai Daukaka. Addinin Musulunci ya watsu yayin da aka ci kasashe da yaki, al'ummai masu wayewa da falsafar jahiliyya kamar su Farisa da Hindu da Sin, sun shigo Musulunci. Haka nan mutane mabiya karkatattun addinan Kiristanci da Yahudanci wadanda kuma sun sami tasirin falsafa da akidojin Kiristanci da Yahudanci su ma sun shigo Musulunci. A hada da abin da aka debo daga tunani da falsafar Yunaniyawa da masu kama da su. Duk wannan ya tsirar da jayayya da shakku, sannan karairayi da bakin manufofi suka shigo akidar tauhidi, yayin da wannan wayewar mai rusawa ta kutsa kai, sai aka samu cewa akidar tauhidi ta kada ta yi rauni a wajen wadanda suka shagalta da bahasi kan akida da ilmin falsafa. Matsaloli da suka shafi rawar da dan'Adam yake takawa a ayyukansa kamar su Jabr (watau tilastawa) da tafwidh (ba da ikon zabi) da kuma Guluwi (masu wuce gona da iri) da tajsim (kudurta cewa Allah jiki ne) da bayani kan Isra'i da Mi'iraji, duk irin wadannan suka taso, da rudani cikin tunanin mutane. Sakamakon haka sai aka sami mazhabobi da kungiyoyi daban-daban suka tsiro tare da akidoji karkatattu, manisanta daga akidar asali ta tauhidi. Wannan ya sa Imaman Ahlulbaiti (a.s) da malamai masu tunani irin na Musulunci sun shiga fagen fama da masu wadannan karkatattun akidu. Jayayyar da har a wannan zamanin gurbinta bai gushe ba, duk da cewa sashin karkatattun kungiyoyin ya bace. Wannan fama da jayay-ya tsakanin wasu kungiyoyi daban-daban ya wanzar da Saboda abin da Allah (S.W.T.) Ya yi baiwa da shi ga Ahlulbaiti (a.s) na tsarkakar fahimta da kewayewa ga dukkan ilmomin shari'a da sanin Allah da kiyayewarsu da ilmin Littafin Allah da na Sunnar Annabi (s.a.w.a), lallai su da mazhabarsu sun taka rawar gani wajen warware rikice-rikice da rusa karkatattun ra'ayuyyuka da kuma kare manufar tauhidi da tsare tsarkinta. Muna da muhawarorin Imaman Ahlulbaiti (a.s) da hadisansu da tafsiran ayoyin tauhidi da bayanansu masu gusar da rudani domin fahimtar Musulunci ta gudana bisa tafarkinta na asali ba tare da karkata ba ko mummunan fahimta wa ayoyin da yi musu tafsiri na son zuciya ko bin wata batacciyar falsafa, karkatacciya. Wannan bayani na Imamai kan fahimtar Littafin Allah da saninsu da Allah (S.W.T.) ya haifar da wani tunani hadadde mai riko da akidar tauhidi.
|