Ahlul Baiti"Bayan Dif (Karbala), ba a cutar da mu kamar cutarwar Fakh ba ([238])". Akwai misalai masu yawa na yunkuri da goyon bayan Ahlulbaiti (a.s) gare su, har wannan (yunkurin) ya zama tafarki da salo na aikin siyasa wanda yake da goyon bayan shari'a. (4). Gwagwarmaya ta Siyasa: Wannan yana da muhimmancin gaske a rayuwar siyasar al'umma a duk lokacin da azzalumin shugaba ya bayyana ba ya gudanar da hukumce-hukumcen Allah Ta'ala, ba ya kuma tsaifa adalci a tsakanin mutane. Kowane Imami na Ahlulbaiti (a.s) ya shugabanci al'umma a fagen siyasa a zamaninsa, kuma ya kasance shi ne alamar bijirewa azzalumai a zukatan jama'ar musulmi. Wannan kuwa shi ne ya bai wa yunkure-yunkuren da aka yi siffar dacewa da shari'a. Halifofin Banu Umayya da Banu Abbas wadanda tarihi ya yi wa shaidar rashin lizimtar addini da barin adalci sun san irin kimar Ahlulbaiti (a.s) a zukatan musulmi, saboda haka suka bi hanyoyi daban-daban domin su nisantar da kaunar Ahlulbaiti (a.s) daga mutane, hanyoyi kamar su tsoratarwa da kai su kurkuku da kisa da rashawa da mukamai da sauransu. A matsayin misali, Mu'awiyya ya yi tawaye ga Imam Ali (a.s.) ya yake shi duk da cewa shi ne halaltaccen halifa. Baya ga haka kuma, bai tsaya ba sai da ya yaki Imam Hasan (a.s.) ya yi tawaye wa halifancinsa, ya kashe shi da guba a shekara ta hamsin, bayan hijira. (A). Bincike Kan Isnadi: Abin nufi da isnadi kuwa shi ne silsilar maruwaita wadanda suke ruwaito hadisi. A nan malaman su kan tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiyar maruwaitan, suna masu dogaro da ilmul Rijal, wanda yake gabatar musu da sanarwar abin da ya jibinci mutanen da suke maruwaita ne, yana shaidar gaskiya ko rashin gaskiyarsu, ba tare da la'akari da mazhabar da maruwaicin ya fito ba. Idan ya zama abin dogaro kuma gaskiya, sai su karbi ruwayarsa, idan kuwa an yi suka cikin al'amarinsa sai su ture ruwayar tasa. Su ba sa duba kome sai gaskiyar mai ruwaya da kubutarsa a bisa ginshikai tabbatattu. (B). Binciken Matani: Abin nufi da matani shi ne asalin nassi. A nan malamai suna bincike ne kan luggar matani da ma'anarta, kuma suna bincike domin su tabbatar da cewa abin da ya taho a hadisin bai sabawa Littafin Allah ko tabbatacciyar Sunna ko wata hakika tabbatacciya wacce Mai shar'antawa Matsarkaki (Allah) Ya tabbatar da ita a matsayin tabbatacciyar hakika a hankalce ba. Yayin da ingancin isnadi da na matani suka tabbata wajen malamai sai su karbi ruwayar, idan kuwa ba haka ba sai su ture ta, ba ruwansu da cewa a wani littafi daga cikin littattafan hadisi ta zo.
|