Ahlul BaitiManzon Allah (s.a.w.a.) ya karanta wannan aya, sai ya juya ga Ali (a.s.), ya ce: "Na roki Allah da ya sanya shi shi ne kunnenka". Sai Ali (a.s.) ya ce: "Babu wani abu da na ji daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na manta shi([51])". Al-Wahidi ya nakalto cikin Asbabun Nuzul daga maruwaita daga Buraida, cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Allah Ya umurce ni da in kusato da kai, kada kuma in nisantar da kai, cewa kuma in ilmantar da kai, don ka kiyaye, kuma Allah Ya yi alkawarin Zai sa ka kiyaye din. Sai aya ta sauka: "Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye". (6). FadinSa Madaukakin Sarki cewa: (إنَّ الَّذينَ آمَنوا وعَمÙلوا الصَّالÙØَات٠سَيَجْعَل٠لمÙم٠الرَّØْمن٠وÙدًّا) "Hakika wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi aiki na nagari, to (Allah) Mai rahama Zai sanya soyayya a tsakaninsu". (Surar Maryam, 19: 96) Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa Aliyu (a.s.) cewa: "Ya Aliyu ka ce: "Ya Allah Ka sanya mini wani alkawari, kuma Ka sanya mini soyayya cikin zukatan muminai". Sai Allah Ya saukar da wannan ayar dangane da Aliyu (a.s.) ([52]). (7). Fadar Allah Ta'ala cewa:
(إنَّ الَّذينَ آمَنوا وعَمÙلوا الصَّالÙØَات٠أÙولئكَ Ù‡Ùمْ خَيْر٠البَرÙيَّة)
|