Ahlul BaitiAn samu daga Ayyub bn Rashid daga Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ya ce: "Abin da bai dace da Alkur'ani ba daga cikin hadisai kyalkyali ne kawai([122])". An samu daga Imam Sadik (a.s.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Wanda ya yi riko da Sunnata yayin sassabawar al'umma, yana da ladan shahidai dari([123])". Wani mutum ya taho wa Amirul Muminina (a.s) ya ce: "Ka ba ni labari (mece ce) Sunna da bidi'a da jama'a da kuma rarraba", sai Amirul Muminina (a.s) ya ce da shi: "Sunna ita ce abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya sunnanta, bidi'a kuma ita ce abin da aka fare shi a bayansa. Jama'a ita ce wadanda suke tare da gaskiya ko da su kadan ne, rarraba kuwa ita ce wadanda suke tare da bata, ko da kuwa suna da yawa([124])". Har ila yau, Imam Ali (a.s) yana cewa: "Sunna biyu ce: Sunna ta wajibci, riko da ita shiriya ce, barinta kuwa bata ce. Da kuma Sunna cikin abin da ba wajibi ba, riko da ita falala ce, barinta kuwa kure ne([125])". Imam Bakir (a.s.) yana cewa: "Ita Sunna ba a yi mata kiyasi, to ya ya za a yi kiyasin Sunna alhali mace mai haila tana rama azumi, amma ba ta rama salla([126])".
|