Ahlul Baiti



Misalin karkata cikin tawili shi ne fuskartar da ayoyin Alkur'ani da sashen masu falsafa da ilimin kalami suka yi bayan sun riga sun yi imani da tunani da mazhabobin kalami da falsafa sannan suka tankwara ma'anonin ayoyin zuwa wadannan mazhabobin.

Misali kuma shi ne cewa akwai abin da sashen marubuta da masu tafsiri ke yi na fuskantar da ayoyin Alkur'ani domin su dace da nazarce-nazarcensu na ilimin kimiyya da tunaninsu na tattalin arziki da zamantakewa da siyasa wadanda marubuta da amsu nazari suka bijiro da su suka kuma yadu a zamanin wadannan masu fassara. Suna bin fadar masu nazarce-nazarcen nan ba tare da akwai wata dangantaka ta hakika ko dacewa ta gaskiya ba. Haka nan muke samun yadda ake murda ayoyi zuwa son zuciya, ko ka ga mai tafsiri ya yarda da wasu ra'ayoyi sannan daga baya ya karkata ayoyin Alkur'ani zuwa ra'ayoyi da halaye da dama, tun da can da kuma ma yanzu.

Hakika masu tafsiri da yawa sun fada cikin wannan kuskuren, kuma daga mazhabobi daban-daban, na Ahlussunna ne ko na Shi'a ko kuma waninsu. Bayan sun yi wannan kuskuren sai su dora kawo hujjoji da dalilai don kare wadannan ra'ayoyi nasu.

Idan muka koma ga tafarkin Musulunci na asali wajen tafsiri za mu ga cewa ya yi watsi da wannan tafarki da muka fadi a baya da kuma tabbatar da asasai ingantattu na tafsiri.

Don kuwa tafsiri kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi, kuma tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da duk wanda ya bi tafarkinsu ba tare da karkata ba da malaman tafsiri masu lizimta, yana da asasai da ginshikansa wadanda suke shiryar da mai tafsiri da mai bincike zuwa dacewa mayalwaciya.

Bari mu kawo bayanin da ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da Imamai Masu shiryarwa (a.s.) da malaman al'umma kan batun sanya ginshikai wadanda ba su da wata karkata, domin tafsiri da tabbatar da ma'aunai da kuma dokoki masu kiyaye wannan ilmi mai daraja, domin shi ilmi ya ba da gudummawarsa tare da cikakkiyar kula da kubuta daga karkatarwa. Kuma domin wannan ilmi ya wadatar da duniyar dan'Adamtaka da ma'anoni da tunani da fahimce-fahimcen da za a iya riska da kuma hukumce-hukumce, ba tare da wata tawaya ko kirdado ko jidali ko bin ra'ayi ko kuma tankwara tafsirin domin ya bi son zuciya ba.

Allama Dabrisi ya ambata cewa: "Ya inganta daga Annabi (s.a.w.a), ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) cewa: "Tafsirin Alkur'ani ba ya halatta sai da asari (wato hadisi) ingantacce da kuma nassi bayyananne([112])".

Lalle Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna bin wannan hanyar, suna kuma watsi da yi wa Alkur'ani tafsirin da ya yi nisa daga wadannan ginshikai guda biyu, wato:

1.  Tafsirin Alkur'ani da Alkur'anin, wato wasu ayoyi su yi wa wasu tafsiri.

2.  Tafsirin Alkur'ani da ruwayoyi da kuma hadisai ingantattu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next