Ahlul BaitiSaboda haka, lallai tushen rudanin shi ne batun isdilahi (yadda ake amfani da kalmomi) da ma'ana ta lugga a wancan zamanin, wadda ma'anar da mutane suke dauka a cikinsa, yanzu ba a daukar ta a wannan zamanin. Sannan kuma Imam ya bayyana ma'anar wannan Mus'haf din domin ya kau da rikitarwar da ka iya faruwa, inda ya ce: "Babu wata aya ta Littafin Allah a cikinsa". Ma'ana, shi ba Alkur'ani ba ne, ba kuma daga Alkur'ani yake ba, ba kuma wahayi ne ba, (shi dai shifta ce ta Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma (rubutun Imam Ali). Wasu malumma suna cewa wannan Mus'hafin wasu tarin addu'oi da shiryarwa ne wadanda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi shiftar su ga Fadima al-Zahra (a.s.) domin tarbiyyarta da kuma ilmantar da ita. To wannan yana bayyana mana kuskure, rudani da jirkitarwa da wasu daga cikin musulmi suka yarda da shi a dalilin mummunar fahimta da mugun nufi. Wanda duk ya yi bitar ruwayoyi da hadisan da suka zo ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) ya kuma karanci tarihin rayuwarsu da alakarsu da Littafin Allah, ba zai sami muhimmanci da kulan da Ahlulbaiti (a.s) suke bayarwa fiye da wanda suke bai wa Littafin Allah, Mai Girma da Daukaka ba, ko a yanayin rayuwarsu ko cikin abin da suka ruwaito da maganganunsu ko cikin abin da suka yi wasiyya ko suka tarbiyyantar ko suka fuskantar da mabiyansu da almajiransu da daukacin 'ya'yan musulmi. Imam Ja'afar Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ya ku mutane, lalle kuna gidan dako ne, kuma kuna kan tafiya, tafiyar kuwa tana sauri da ku, kun ko ga dare da yini da rana da wata suna tsufar da kowane sabon abu, suna kuwa kusanto da kowane manisanci suna kawo kowane abin alkawartawa, to ku tanadi shiri wa tafiyar nan mai tsawo". Ya ce: sai Mikdad bn Aswad ya mike, ya ce: Ya Manzon Allah! Mene ne gidan dako?, sai ya ce masa: "Gidan isarwa da yankewa, to idan fitinu kamar yankin dare mai duhu sun rikitar da al'amurra a kanku, na hore ku da Alkur'ani, domin shi, mai ceto ne abin karbawa ceto, mai jayayya abin gaskatawa. Duk wanda ya sanya shi gabansa zai ja-gorance shi zuwa aljanna, wanda ko ya sanya shi a bayansa zai iza shi zuwa wuta. Shi kuwa ja-gora ne mai shiryarwa zuwa mafi alherin hanya. Kuma shi littafi ne wanda a cikinsa akwai rarrabewa da bayani da riba (ko karuwa) shi ne rarrabewa kuma ba kakaci ba ne, yana da baya da ciki. Bayansa hukumci ne, cikinsa kuwa ilmi ne, bayan nasa gwanin kyau ne da shi, cikin nasa kuwa zurfi ne da shi. Yana da taurari, bisa taurarinsa ma akwai wasu taurarin. Ba a iya kididdigar ababen ban mamakinsa, abubuwan ban sha'awarsa kuma ba sa tsufa. Akwai fitilun shiriya da hikima cikinsa, kuma mai shiryarwa ne zuwa ga masaniya ga wanda ya san sifa. To mai yawo ya yi yawo (cikin Alkur'ani) da ganinsa, kuma dubinsa ya riski sifar domin ya tsira daga halaka ya kuma kubuta daga tsanani. Domin kuwa tunani rayuwar zuciya mai gani ne, kamar yadda mai tafiya cikin duhu yake haskaka hanya da haske. To na hore ku da kubuta mai kyau da karancin dako([98])".
|