Ahlul Baiti6. Imam Ja'afar bn Muhammad Sadik (a.s.), wanda ake danganta mazhabar Ja'afariyya Imamiyya gare shi, an haife shi a shekara ta 83 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 148 bayan hijira. 7. Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s.), an haife shi a shekara ta 128 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 183 bayan hijira. 8. Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s.), an haife shi a shekara ta 148 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 203 bayan hijira. 9. Imam Muhammad bn Ali al-Jawad (a.s.), an haife shi a shekara ta 195 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 220 bayan hijira. 10. Imam Aliyu bn Muhammad al-Hadi (a.s.), an haife shi a shekara ta 212 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 254 bayan hijira. 11. Imam Hasan bn Ali al-Askari (a.s.), an haife shi a shekara ta 232 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 260 bayan hijira. 12. Imam Muhammad bn Hasan al-Mahdi (a.s.), an haife shi a shekara ta 255 bayan hijira, yana kuma raye a boye gwargwadon abin da ruwayoyi suka kawo. Mun riga da mun yi magana kan guda uku na farko (wato Aliyu, Hasan da Husaini), mun san matsayi da mukaminsu cikin Alkur'ani da Sunnar Annabi (s.a.w.a), wadanda suke nuni da wajibcin yin musu da'a da kuma karba daga gare su. To yanzu kuma bari mu yi bibiyar zantuttukan malamai dangane da sauran da suka saura daga cikin wadannan taurari masu albarka na gidan Annabci. 4- Imam Aliyu bn Husain (Zainul Abidin) (a.s.):
|