Ahlul Baiti"Hakika sanannen zancen Imamiyya kan ragi a cikin Alkur'ani shi ne rashin hakan a cikinsa", har ila yau ya ce an samu daga Shaikh Ali bn Abdul Ali cewa shi ya wallafa littafi na musamman kan kore tawaya cikin Alkur'ani daga hadisai, inda ya ce idan hadisi ya zo bisa sabanin dalili na Littafin Allah da Sunna ingantacciyar ko kuma ijma' (abin da malamai suka hadu a kai amma da sharadin akwai wani Imami a cikinsu), kuma ba zai yiyu a yi masa wani tawili ba ko kuma daukansa da wasu ma'anoni ta wasu fuskoki ba, to wajibi ne a jefar da shi([94])". Marigayi Allama kana Mujahidin zamani Shaikh Muhammad Husain Kashif al-Ghida ya fada cikin littafinsa mai suna Aslul Shi'a wa Usuluha cewa: "Lalle wannan Littafin da yake hannu musulmi shi ne Littafin da Allah Ya saukar masa (Annabi) domin gajiyarwa da kalubale, da kuma cewa babu nakasi a ciki, babu jirkita, babu kuma kari, a kan hakan ne (malamai) suka hadu a kai". Sharifi mai kira zuwa ga gyara, Sayyid Abdul Husain Sharafuddin ya fada cikin littafinsa Fusulul Muhimma fi Talifil Umma cewa: "Alkur'ani mai hikima, barna bata zuwa masa a zamaninsa ko a bayansa. Abin sani dai shi ne a cikin bangwaye biyun nan, shi ne kuma a hannun mutane, ba a kara ko da harafi ko kuma a rage wani ba, babu musayyar kalma da wata, ko harafi da wanin harafin. Kuma ko wani harafi cikin haruffan Alkur'ani tabbatacce ne a kowani zamani tun daga zamanin da aka saukar da shi. Sannan ya kasance a tare a wancan zamani mafi tsarkaka, yana rubuce kamar yadda yake a yau. Mala'ika Jibrilu (a.s.) ya kasance yana kawo shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.) sau da yawa, dukkan wannan yana cikin al'amurra sanannu wajen masu bin diddigi cikin malaman Imamiyya. Don haka ba a dogara da maganan 'yan Hashawiyya, domin su ba su da fahimta". Haka nan kuma malamin nan mai yawan bincike, babban mutum, Sayyid Muhsin Amin Husaini Amili ya fadi cikin littafinsa A'ayanu al-Shi'a cewa: "Babu wani daga cikin 'yan Imamiyya, dadadde ko na yanzu da yake cewa akwai kari, babba ne ko karami, cikin Alkur'ani, face ma dai dukkansu sun hadu a kan rashin kari, hakika wadanda ake dogaro da maganarsu daga cikin masu bin diddigi sun hadu a kan cewa babu abin da ya ragu daga cikin Alkur'ani". To wannan dai shi ne Alkur'ani mai girma da kuma ra'ayin Imamiyya dangane da shi, shi ne kuma dai a yanzu yake hannu musulmi, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya zo da shi. Kuma shi mai wanzuwa ne da wanzuwar dan'Adam a kan doron kasa, yana haskaka wa dan'Adam hanyar rayuwa, ya kuma rike hannun al'umma zuwa ga shiriya. Malamai da masu bincike da masu bin diddigi, suna ganin cewar abin da ke yawo tsakanin wasu mutane na ruwayoyi da zantattuka (marasa tushe) da suke maganar tawayar Alkur'ani, cikin da'irar Ahlussunna da Shi'a, ba kome ba ne face sanyawa ce ta makaryata, wacce babu makawa dole a yi jifa da su. Haka nan ana samun wasu ruwayoyi wadanda ana yiwa zahirinsu wata fahimta ba tare da zurfafa nazari wajen karanta su da fahimtar su ba, wacce kuma ta sa ake cewa da akwai tawaya cikin Alkur'ani ko kuma samuwar wani Mus'hafi daban kamar yadda al'amarin ya rikitar da wasu mutane, masu muzanta Musulunci kuma suka dauki hakan wata dama ce gare su ta musguwa wa Musuluncin da kuma musulmai da kuma kokarin kawo rarrabuwa tsakaninsu. Kamar abin da aka ruwaito daga Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.), ba tare da kula da ingancin ruwayar ko rashin sa ba. Ga abin da ya ce:
|