Ahlul BaitiImam Sadik (a.s.) yana cewa: "Mahaddacin Alkur'ani, mai aiki da shi yana tare da Mala'iku Marubuta, Masu daraja, Masu da'a ga Allah([99])". Imam Aliyu bn Husain (a.s.) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:"Wanda Allah Ya ba shi Alkur'ani, sai ya ga cewa an bai wa wani mutum fiye da abin da aka ba shi, to hakika ya rena babban abu, ya kuma girmama karami([100])". Ya zo kuma daga wajen Imam Muhammadu Bakir (a.s.) cewa ya ce Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ya ku jama'a makarata Alkur'ani! Ku ji tsoron Allah Mai Girma da Daukaka cikin abin da Ya dora muku na LittafinSa domin ni abin tambaye ne, ku ma abin tambaya ne. Ni za a tambaye ni kan isar da sako, ku kuma za a tambaye ku ne kan abin da aka dora muku na Littafin Allah da Sunnata([101])". Sannan kuma Imam Sadik (a.s.) yana cewa: "Ya kamata mumini kada ya mutu har sai ya koyi Alkur'ani, ko kuwa yazama cikin koyonsa([102])". Imam Sadik (a.s.) kuma yana cewa:"Alkur'ani alkawarin Allah ne da bayinSa, to hakika ya kamaci mutum musulmi ya yi dubi cikin alkawarinsa, ya kuma karanta ayoyi hamsin daga ciki a kullum([103])". Imam Sadik din dai yana cewa: "Abubuwa uku za su kai kuka zuwa ga Allah Madau-kakin Sarki: masallacin da aka kaurace masa ba a salla a cikinsa, malamin da ke tsakanin jahilai da kuma Alkur'anin da aka rataye shi kura tana hawa kansa don ba a karanta shi([104])".
|