Ahlul Baiti[54] Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30. [55] Al-Ithafu bi hubbil Ashraf na Abdullah bn Muhammad bn Amir al-Shabrawi al-Shafi'i, shafi na 21. [56] Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'ir al-Ukba fi Manakib Zawil Kurba, shafi na 30. [57] Zakha'irul Ukba na Dabari, shafi na 67. [58] Dabari ya ruwaito wannan hadisi da dan bambancin lafazi cikin Mu'ujamul Kabir, juzu'i na 1 shafi na 24, haka nan cikin Kanzul Ummal juzu'i na 6 shafi na 220, Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba shafi na 121, da Suyudi cikin Ihya'ul Mayyiti shafi na 29, da wannan lafazi" "Dabarani ya fitar da shi daga Umar, cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Dukkan wani mutum, to danganta-karsa tana komawa ne ga mahaifinsa, in ban da 'ya'yan Fadima, don dangantakarsu tana komawa ne gare ni, ni ne mahaifinsu". [59] Tirmizi ya ruwaito shi cikin Sahihinsa juzu'i na 2, shafi na 380 da isnadinsa daga Zaid bn Arkam, haka ma Hakim ya ruwaito shi cikin Al-Mustadrak juzu'i na 3 shafi na 109, shi ma daga Zaid bn Arkam, haka nan ma Ahmad bn Hambal ya ruwaito shi cikin Musnad dinsa daga Abu Sa'id al-Khudri, juzu'i na 3 shafi na 17, kamar yadda kuma Dabarani cikin Mu'ujamul Kabir juzu'i na 1 shafi 129 ya ruwaito, haka ma Muhibbuddin Dabari cikin Zakha'irul Ukba daga Ahmad shafi na 16. [60] Al-Ithafu bi hubbil Ashraf, shafi na 22. [61] Kamar na sama. [62] Kamar na sama, shafi na 22-23. [63]Al-Balagi cikin Ala'ur Rahman shafi na 44. Allama Faiz Abadi ya nakalto cewa: " Muslim ya ruwaito Hadisus Sakalain cikin sahihinsa, haka ma Ahmad bn Hambal cikin Musnad dinsa, juzu'i na 4 shafi na 366, da Baihaki cikin Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 148, juzu'i na 7 shafi na 30, haka ma Darimi ya ruwaito shi Sunan dinsa, juzu'i na 2 shafi na 431, Al-Muttaki cikin Kanzul Ummal, juzu'i na 1 shafi na 45, da juzu'i na 7 shafi na 102, haka ma Dahawi cikin Mishkilul Athar juzu'i na 4 shafi na 368, Tirmizi ma ya ruwaito shi cikin Sahihinsa, juzu'i na 3 shafi na 109, haka Nisa'I cikin Khasa'is shafi na 21. Haka nan ma cikin al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3 shafi na 148.
|