Ahlul Baiti"Imam Sadik (a.s.) ya la'ance shi ya ce: 'shi makahon zuciya ne da idanu([198])'. Kamar yadda kuma Imam din ya la'anci Abu Mansur al-Ajli, daya daga cikin 'yan Gullatu, an ruwaito cewa: 'Al-Kishshi ya kawo cikin Rijal dinsa shafi na 300 cewa Imam Sadik ya la'ance shi sau uku. Sannan kuma Yusuf bn Umar al-Thakafi, gwamnan Iraki, ya tsire shi a zamanin Hisham bn Abdul Malik([199])'. Hakika Imam Sadik (a.s.) ya bayyana matsaya kan wadannan 'yan gullatu, daga nan ya ambaci wasu daga cikinsu, su ne: Mughira bn Sa'id, Bazi, Sirri, Abul Khaddab Muhammad bn Abi Zainab al-Ajda', Mu'ammar, Bashshar Sha'iri, Hamza Barbari da Sa'id Nahadi, sai ya ce: "Allah Ya la'ance su, mu dai ba mu rabuwa da makaryata msu yi mana karya ko kuma wani mai gurgun tunani. Allah Ya isar mana ga dukkan makaryaci, Ya kuma dandana musu zafin karfe([200])". A wani hadisin kuma Imam Sadik (a.s.) ya barranta daga 'yan Gullatu, inda yake cewa: "Ya ku jama'ar Shi'a - shi'ar Alu Muhammadu- ku kasance matsakaita, wadanda suka wuce gona da iri (masu guluwi) su dawo gare ku, wadanda kuwa suka yi nawa su risko ku". Sai wani mai suna Sa'id ya ce: 'Allah Ya sanya ni fansarka! Wane ne mai guluwi? Sai Imam ya ce masa:"Wasu mutane ne masu fadi game da mu, abin da mu ba mu fada ba, wadannan ba su daga gare mu, mu ma ba mu daga gare su". Sai mutumin ya ce: 'To wane ne mai nawa? Sai ya amsa masa da cewa: "Shi ne mai bidar (gaskiya) yana nufin alheri, alherin zai same shi kuma za a sakanta masa da shi([201])". Daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa yayin da Imam din ya sami labarin cewa Abul Khaddab na wuce gona da iri sai idanunsa suka cika da hawaye yana cewa: "Ya Ubangiji, na barranta ya zuwa gareKa, daga abin da Al-Ajda yake ikirari a kaina, gashina da fatar jikina sun ji tsoronKa. Ni bawa ne a gare Ka dan bawanKa, makaskanci mai tawali'u".Daga nan sai ya sunku'i da kai na dan lokaci kamar yana ganawa da wani abu, sai ya daga kansa yana cewa:"Haka yake, haka yake! Bawa mai tsoro, makaskanci gaba ga Ubangijinsa, kankani, mai tsananin tsoro. Wallahi ina da Ubangijin da nake bautarSa, bana yi masa tarayya da kome. Me ya same shi (Abul Khaddab)? Allah ya kunyata shi, Ya zuba masa tsoro. Kada kuma Ya ba shi aminta daga firgici a ranar kiyama…..ba haka amsawar Annabawa take ba, ko ta mursalai, ba kuma amsawa ta ba. Amsawa ta kam ita ce fadar cewa: Ya Allah na amsa maKa, na amsa maKa Ya Allah ba Ka da abokin tarayya([202])". Sadir ya ce: 'Na ce da Abu Abdullah (a.s.) cewa wasu mutane suna ikirarin cewa ku alloli ne, suna kuma kafa hujja da fadar Allah (S.W.T.) cewa:"Kuma Shi ne Wanda ke abin bautawa a sama, kuma bautawa a kasa"", (Surar Zukhruf aya ta 84),sai ya ce:"Ya kai Sadir! (Ka sani) jina da ganina da fatata da namana da gashina duk sun barranta daga wadannan mutane, Allah ma Ya barranta da ga gare su. Ba kan addinina wadannan suke ba, ba kuma kan na iyayena ba. Na rantse da Allah ba zai tara ni da su ba ranar lahira, kuma ba su zo a wannan rana ba face Allah Na fushi da su([203])".
|