Ahlul Baiti



Haka nan kuma Imamai (a.s.) sun yi watsi da ra'ayin masu cewa an sakarwa mutum akala sai yadda ya ga dama zai yi, ba tare da Allah Yana iya hana shi ba. Sun bayyana cewa wannan ra'ayi karkatacce da cewa tuhumar Allah ne da rashin cikakken iko kan bayinSa da gajiyawarSa kan hakan. Alhali kuwa Allah (S.W.T.) Mai cikakken iko ne, kuma Mamallakin dukkan halittunSa.

Imamai (a.s.) suna da matsaya matsakaiciya dangane da al'amarin da ya shafi adalcin Ubangiji. Wannan matsaya tana kore Tilastawa da Sakarwa, tana cewa: (Nufin mutum baya iya rabuwa da nufin Allah). Sun bayyana wannan alakar da take tsakanin nufin mutum da nufin Ubangiji bayani cikakke a akidance. Nan gaba za mu kawo ruwayoyinsu masu nuna wannan ra'ayi.

Kafin mu kawo wadannan ruwayoyi, bari mu yi dan sharhi kan batutuwan da mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bambanta da masu ra'ayoyi kan mas'alar adalcin Allah, bisa abubuwa guda uku na asasi:

Dan'Adam yana da nufi da ikon zabin duk aikin da zai yi, ko na alheri ko na sharri, haka kuma kin aikata shi. Mutum yana iya kisan kai ko sata ko zalunci ko karya, da wannan nufin da ikon da yake da shi. Haka kuma yana da daman tsai da adalci da aikata aikin kwarai da yin salla da barin haramtattun abubuwa, da wannan nufi nasa da iko.

Hakika Allah (S.W.T.) Yana da ikon hana mutum kowane aiki, kamar yadda yake da ikon sa mutum aikata kowane aiki ba tare da zabin mutum ya sami tasiri ba. Sai dai Allah ba Ya tilastawa kowa aikata alheri ko sharri.

Amma Shi Allah, domin tausayinSa da jin kanSa, Yana shiga tsakanin bawan da ya cancanci taimakonSa wajen aikata mummunan aiki, domin jin kai. Haka ma Yana taimaka masa wajen aikata alheri idan ya cancanci taimakon.

1.  Wani abin da yake da dangantaka da adalcin Ubangiji kuma shi ne: Allah Yana sakantawa kowane mutum ranar kiyama da abin da ya aikata, alheri ko sharri. Sai dai kuma wata kungiyar ta musulmi tana ganin cewa mai yiyuwa ne Allah Ya shigar da mai kyautata aiki cikin wuta, mai mummunan aiki kuma aljanna, suna kuma dogara ne, bisa kuskure da mummunan fahimta, kan wannan aya mai girma: "Ba a tambayarSa ga abin da Yake aikatawa, alhali kuwa su ana tambayarsu". (Surar Anbiya, 21: 23)

Wasu jama'a daga cikin musulmi sun dogara da wannan ayar ne bisa tafsiri na kuskure, suka ce ba ya wajaba kan Allah (S.W.T.) Ya cika alkawarin sakayya da Ya yi a ranar kiyama. Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun mai da martani kan wannan zance da cewa, wannan ya sabawa gaskiyar Allah Ta'ala da adalcinSa.

Wancan ra'ayin yana daidaita mai kyautatawa da mai mummunan aiki, hakan kuwa yana rusa kimar kallafawa bayi da kuma sanya shari'a. Ingantaccen zance dai shi ne babu wani aikin da ba shi da sakamako, ko kuma mai daukar laifin yinsa, kamar yadda aya ta ce:

"To wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai ganshi. Kuma Wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next