Ahlul Baiti



Daga cikin abin da Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci da shi ga wani mabiyinsa, Abu Usama ya kuma umurce shi da ya isar da shi ga sauran mabiyansa, shi ne cewa:

"Ku ji tsoron Allah ku kasance ado a gare mu, kada ku zamo abin kyama. Ku janyo mana dukkan soyayya, ku ije mana duk wani mugun abu, domin mu ba kamar yadda aka fada dangane da mu muke ba. Muna da hakki cikin Littafin Allah da dangantaka da Manzon Allah (s.a.w.a.) da tsarkakewa daga Allah, da haifayya tsarkakakkiya, ba mai ikirarin hakan, koma bayanmu, face makaryaci*. Ku yawaita ambaton Allah da tuna mutuwa da karatun Alkur'ani da salatin Annabi (s.a.w.a) domin akwai (ladan) kyawawan aiki goma ga ko wane salati a gare shi([207])".

Imam Sadik (a.s.) ya yi wasicci wa Isma'il bn Ammar, daya daga cikin sahabbansa, da cewa: "Ina ma wasicci da tsoron Allah da tsantseni da gaskiya cikin magana da mai da amana da kyautatawa makwabta da yawan sujada, don da wannan ne Annabi (s.a.w.a) ya umurcemu([208])".

Hisham bn Salim ya ce: 'Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana fada wa Hamran cewa:

"Ka dubi wanda ya kasa ka, kada ka dubi wanda ya fi ka, domin haka ya fi (tabbatar da) wadar zuci ga abin da aka yanka maka, kuma za ka fi cancantar kari daga Allah. Ka sani cewa kadan na dawwamammen aiki wanda aka yi yakini, a wajen Allah, ya fi mai yawa dawwamamme amma babu yakini a cikinsa. Ka sani cewa babu tsantsenin da ya fi nisantar ababen da Allah Ya haramta, da kuma kamewa ga barin cutar da musulmai da yi da su. Babu kuma abin da ya fi kyan hali faranta rai. Kuma babu dukiyar da tafi amfani daga wadatuwa da kadan mai biyan bukata. Babu jahilcin da ya fi jiji da kai daci([209])".

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a.) kan siffofin muminai cewa:

"Wanda ya yi bakin cikin mummunan aikinsa, ya yi farin ciki da kyakkyawan aikinsa, to mumini ne([210])".

Wadannan bayanai suna nuna siffar mumini mai riko da addini irin wanda Ahlulbaiti (a.s) suka yi kokarin samarwa kuma wannan shi ne tafarkinsu na tarbiyyar al'ummar musulmi. Shi ne kuma kiran da suka yi wa al'ummar Annabi (s.a.w.a) na lizimtar Littafin Allah da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.) da gina rayuwa bisa wannan shiriya da tafarki mai karfi. Babu abin da ya fi dacewa ga musulmi sai bin shiryarwarsu da wasiccinsu da kuma wa'azinsu.

Gudummawar Ahlulbaiti (a.s) A Fagen Siyasa

Babu shakka al'ummar musulmi ta san matsayin Ahlulbaiti (a.s) da hakkinsu a kan wannan al'umma na shugabantarta. Domin haka ne za a iya ganin cewa Ahlulbaiti (a.s) suna matakin kololuwa a fagen siyasa da shugabancin Musulunci, domin su shiryar da al'umma, su tabbatar da gyara da aiwatar da hukumce-hukumcen addini da tsayar da adalci.

Duk wanda ya karanci tarihin Musulunci zai gani a sarari cewa shugabantar al'umma bayan zamanin Khulafa'u al-Rashiduna ta koma mulukiyya mai dora kanta bisa bayin Allah da jan hankulansu da dukiya da mukamai da kuma dankwafe hukumce-hukumcen shari'a da wasa da su. Wannan wasa da shari'a da makomar al'umma ya janyo sassabawa da juyin-juya-hali da jayayya mai tsanani da zubar da jinin kungiyoyi masu sabanin ra'ayoyi da tunace-tunace masu warware juna sun zama sakamakon wannan. Wasunsu suna goya wa sarakuna baya kan zaluncinsu da kuma horar da mutane su mika wuya da hana su bijirewa da warware mubaya'arsu ga azzalumai. Wasu kuma sun yi amfani da wannan damar (ta jayayya tsakanin musulmi) wajen tabbatar da mugun nufinsu na ruguza addini yayin da suka dora kira da halalta dukkan haram da dukiyoyi da mata da rusa wajibai, kungiyoyi irinsu 'yan Karamida, Mazdakiyya da Kharmiyya da dai sauransu. Wasu kuma suka dora kira zuwa ga rudani da rusa dukiyar hukuma da zubar da jini da kafirta kowa da kowa kamar su Khawarijawa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next