Ahlul Baiti6- Wasu Ruwayoyi Na Daban Kamar dai yadda muka bayyana, hadisai da ruwayoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) game da Ahlulbaitinsa (a.s.) suna da yawan gaske, kuma ba za su kidayu ba a wannan karamin littafin. Malamai da masu hadisi sun kebance musu litattafai, ko kuma fasulla a littattafan hadisai, ko kuma sun ambata a wuraren da suka dace cikin litattafan tafsiri da ruwaya. Ga kadan daga ciki: "Mu Ahlulbaiti ba a gwada mu da kowa([81])". A cikin wannan hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mukamin Ahlulbaiti (a.s) ne, da kuma matsa-yinsu madayanci, domin ya sanar da al'umma mahal-linsu, ya kuma shiryar da ita zuwa ga riko da su da lizimtar hanyar su a bayansa, domin a auna su da wasu wadanda ba su ba, don a gani. A cikin wani hadisi na daban kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana magana ne kan Ahlulbaitisa (a.s.), inda yake cewa: "Mu Ahlulbaiti, Allah Ya zaba mana lahira bisa ga duniya, kuma lalle Ahlulbaitina za a nuna musu son kai da tsanani da kora cikin garuruwa, har wasu mutane za su zo ta nan - sai ya yi nuni da hannunsa ta gabas - ma'abutan bakar tuta, za su tambayi hakki, ba za a ba su ba, za su yi yaki kuma su yi nasara. Za a ba su abin da suka so kuma ba za su karbe shi ba har su mika ta (tutar) ga wani mutum daga Ahlulbaitina, har sai ya cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci. To duk wanda ya riski wannan ya taho musu ko da da jan ciki ne a kan kankara([82])". (Dailami ya kawo hadisi daga Abu Sa'id (r.a.) cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Fushin Allah ya tsananta kan wanda ya cutar da ni dangane da Ahlulbaitina([83])". (Daga Aliyu (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ku yi wa 'ya'yanku tarbiyya kan halaye guda uku: son Annabinku da son Ahlulbaitinsa da kuma karatun Alkur'ani, domin mahaddatan Alkur'ani na cikin inuwar Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa, tare da AnnabawanSa da ZababbunSa([84])"). (Dabarani ya ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) yana cewa: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
|