Ahlul Baiti



"Za a kashe ka, saboda haka ka tsananta yaki domin mutanen fasikai ne, suna bayyana imani suna boye munafunci da shirka. Lalle ne mu daga Allah muke kuma wajenSa za mu koma! Ga Allah nake neman ladan rashinku ([234])".

Yayin da Husain ya yi shahada aka kawo kawukan wadanda suka yi shahada tare da shi wajen mahukuntan Abbasiyawa, sai aka tambayi Imam Kazim cewa wannan kan Husaini ne? sai ya ce:

"E, lalle ne mu ga Allah muke, kuma lalle ne mu zuwa gare Shi za mu koma. Na rantse da Allah, ya mutu musulmi ne salihi, mai yawan azumi, mai umurni da kyakkyawa, mai kuma hana mummuna, babu tamkarsa cikin mutanen gidansa ([235])".

Shi dai Husain ya kasance ne yana kiran mutane da cewa:

"Ina kiranku ne zuwa ga abin da Alu Muhammadu suka yarda da shi, da aiki da Littafin Allah da sunnar Annabi (s.a.w.a) a tsakaninku, da kuma tsayar da adalci a tsakanin jama'a([236])".

Kiran da Husain ya yi, kira ne zuwa ga biyayya ga mutumin da ya cancanci shugabanci, wanda yake daga Alu Muhammadu, kuma shi ne Imam Kazim (a.s.), kamar yadda Zaid ya yi nufin mai da shugabanci ga Imam Sadik (a.s.) da ya yi nasara.

Hakika halifan Abbasiyawa ya fahimci goyon bayan da Imam Kazim (a.s.) yake yi wa yunkurin Husain a yakin Fakh.

Allamah Majilisi ya ruwaito cewa:

"Sai ya (halifan Abbasiyawa) ci gaba da zagin Dalibiyawa (jikokin Ali bn Abi Talib) har ya ambaci Musa bn Ja'afar (a.s.), sai ya zage shi yana cewa: 'Wallahi Husaini bai yunkura ba sai da umarninsa (Musa bn Ja'afar), ba abin da ya bi face abin da yake so domin shi (Imam Kazim) ne ma'abucin wasiyya a cikin mutanen wannan gidan. Idan na bar shi, Allah Ya kashe ni ([237])".

Imam Jawad, jikan Imam Kazim (a.s.) shi ma ya bayyana tasa matsayar dangane da masu gwagwarmar, inda ya ce:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next