Ahlul BaitiMalikawa kuwa sun ce: Wasiyya tana inganta wa cikin da yake samamme ne da wanda zai samu nan gaba, domin suna ganin halalcin wasiyya wa wanda ba samamme ba. (Dubi Tazkiratul Hilli da Fikihu ala Mazahib Al-Arba' da litattafan fikihu na Hanbaliyya da dama a babin wasiyya). Wadannan misalai ne 'yan kadan daga fikihu idan an kwatanta mazhabobin Musulunci da junansu. Muna iya ganin yadda wasu mazhabobi suka dace ko suka saba da juna a mas'alolin hukumce-hukumce. Za a ga Malikiyya da Shafi'iyya sun dace da Imamiyya, su saba da Hanafiyya da Hambaliyya, ko Hanafiyya ko Hambaliyya su dace da Imamiyya, su saba da sauran mazhabobi Ahlussunna, da dai sauran irin wannan. Saboda haka sassabawa ba ta dogara da kasancewa cikin Sunna ko Shi'a, sassabawar ta ilimi da tunani, ba sabawar Sunna da Shi'a ba ce, ko kusa, sai dai sabawa ce ta tsarin ilmin ciro hukumce-hukumce na mazhabobin nan biyar. Saboda haka ya zama wajibi a kan mu mu tantance dalilai na shari'a ta hanyar tattaunawa ta ilmi domin isa ga dacewa, sabili da hukumcin Allah dai daya ne akan kowace mas'ala. Masu kokarin nuna cewa sabanin da ke akwai tsakanin Sunna da Shi'a tamkar ya mai da su kishiyoyi masu jayayya tsakanin juna, ba abin da suke yi sai karkata gaskiya da nisantar tsarin kubutaccen tattaunawa ta ilmi. Babu abin da suke yi sai aiki wa abokan gaban musulmi ta hanyar wargaza hadin kan musulmi. Musulmi Al'umma Ce Guda "Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gabar rami na wuta, sai Ya tsamar da ku daga gare ta. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku, za ku shiryu # Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma su na hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara # Kuma kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka saba wa juna, bayan hujjoji bayyanannu sun je musu, kuma wadannan suna da azaba mai girma". (Surar Aali Imrana, 3: 103-105) "Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba # Kuma masu mai da al'amari gare Shi kuma ku bi Shi da takawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai # Watau wadanda suka rarrabe addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya, kowace kungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai. (Surar Rum, 30: 30-32) "Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shi ne Allah Ubangijina, a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarina. (Surar Shura, 42: 10) "Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa da ma'abota al'amari daga cikinku. Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. Wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara". (Surar Nisa'i, 4: 59) "Kuma lalle ne wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Ni, Ubangijinku ce, sai ku bi Ni da takawa". (Surar Mu'uminun, 23: 52) "Kuma ku yi da'a ga Allah da MazonSa, kuma kada ku yi jayayya har ku raunana kuma karfinku ya kau, kuma ku yi hakuri, lalle ne Allah Yana tare da masu hakuri". (Surar Anfal, 8: 46)
|