Ahlul Baiti6- Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s.): To batun dansa, Ja'afar al-Sadik (a.s.) kuwa, hakika malamai sun yawaita yabo gare shi da kuma mahaifansa da kuma girmama matsayinsu. Za mu ambaci kadan daga cikin wadannan maganganu, kamar haka: Allama Muhakkik Sayyid Muhsin Amin ya nakalto cewa: "Lallai Hafiz bn Akd al-Zaidi a cikin littafinsa na Rijalu, ya kawo mutum dubu arba'in daga magaskatan da suka ruwaito daga Ja'afar bn Muhammad (a.s.), ban da kuma wadanda ba a tabbatar da gaskiyarsu ba. Ya kuma ambaci rubuce-rubucensu([142])". Ibn Shahr Ashub ya kawo a cikin littafinsa, Manakib Aali Abi Dalib daga littafin Hilyatul Awliya' na Abu Nu'aim cewa: "Hakika manyan malamai da shuwagabanni sun karbi hadisi daga Ja'afar al-Sadik, cikinsu har da: Malik bn Anas, Shu'ba bn Hajjaj, Sufyan al-Thawri, Ibn Jarih, Abdullah bn Amru, Ruh bn Kasim, Sufyan bn Uyaina, Sulaiman bn Bilal, Isma'il bn Ja'afar, Hatim bn Isma'il, AbdulAziz bn Mukhtar, Wahb bn Khalid, Ibrahim bn Dahhan da dai sauransu. Ya ce: Muslim ya fitar da hadisi cikin Sahihinsa yana mai kafa hujja da hadisinsa (Imam Sadik). Wasu kuma suka ce: Wadanda suka ruwaito daga gare shi sun hada da Malik, Shafi'i, Hasan bn Salih, Abu Ayyub al-Sajistani, Umar bn Dinar da Ahmad bn Hambal. Malik bn Anas ya ce: Ido bai ga ba, kunne bai jiba, kuma bai fado wa zuciyar wani mutum wanda ya fi Ja'afar Sadik a falala da ilmi da ibada da tsantsaini([143])". Uztaz Shaikh Mahmud Abu Zuhra, shaihin malami a Jami'ar Azhar ta kasar Masar ya yi magana kan Imam Sadik (a.s.) a cikin gabatarwar littafinsa mai suna Imam Sadik, ya ce: "Bayan haka; hakika mun yi niyyar mu yi rubutu kan Imam Ja'afar Sadik, da taimakon Allah da gamo da katar daga gare Shi. Hakika mun yi rubutu kan bakwai daga shuwagabanni masu daraja, ba mu jinkirta rubutu kansa domin ya kasa wani daga garesu ba, a'a, shi yana da fifikon gabatuwa bisa mafiya yawansu. Yana kuma da fifiko makebanci bisa manya-manya daga cikinsu domin Abu Hanifa ya kasance yana ruwaitowa daga gare shi yana kuma daukarsa a matsayin mafi sanin abin da mutane suka sassaba a kansa, kuma mafi kewayewa da ilmi cikin dukkan fukaha'u. Imam Malik ya kasance mai halartarsa domin karatu da ruwaya. Imam Ja'afar Sadik yana da falalar malanta kan Abu Hanifa da Malik, wannan kuwa ya isa daraja. Saboda wannan, jinkirtawa ba ta yiyuwa domin nakasinsa kuma ba a gabatar da waninsa domin fifiko. Kuma bayan haka ma shi jikan Aliyu Zainul Abidin ne, wanda ya kasance shugaban mutanen Madina a zamaninsa wajen falala da daraja da addini da ilmi, kuma mutane kamarsu Ibn Shihab al-Zuhri da kuma da dama daga cikin tabi'ai sun yi dalibta a hannunsa. Shi ne dan Muhammad Bakir wanda ya tsaga ilmi ya kai ga ainihinsa. Shi yana daga wadanda Allah Ya tattara musu daraja a zatinsu da daraja ta girman asalinsu na dangin Hashimi da kusanci da Annabi (s.a.w.a) ([144])". Amru bn Mukdam ya kasance yana cewa:
|