Ahlul Baiti"Ba za ku shiga aljanna ba sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba sai kun so juna. Shin in shiryar da ku ga wani abu idan kun yi za ku so juna? Ku yada sallama tsakaninku([250])". Irin wadannan kulle-kulle babu shakka aikin manyan azzaluman duniya ne, masu rawar jiki duk san da aka ambaci hadin kan musulmi da gangamin al'ummar Annabi (s.a.w.a), saboda tsantsar karfin ta na mutane da albarkatu da akida mai karfin gaske. Abin da ya dace da malamai da masu tunani da marubuta da masu wa'azi da duk masu daukan nauyin kula da makomar addinin Musulunci masu kyakyawar niyya shi ne su karkata akalar da'awarsu zuwa kalubalantar barnar masu mugun nufi, su kira al'umma zuwa ga hadin kai da warware matsalolinsu na shari'a da tunani bisa dalilai na ilmi. An nakalto daga Ibn Shar Ashub cikin littafinsa Munakib Ali Abi Talib cewa: "Wata mace ta yi wasicci da sulusin dukiyarta don a yi mata sadaka, aikin hajji, a kuma 'yanta bawa, to amma dukiyar ba ta isa dukkan wadannan ayyukan ba. Sai aka tambayi Abu Hanifa da Sufyan Al-Sauri kan hakan, sai kowanensu ya ce: A nemi mutumin da ya yi aikin hajji amma bai cika ba sai a ba shi kudi ya karasa da wanda yake kokarin 'yanta wuya, amma bai gama biya ba sai a cika masa, sannan a yi sadaka da sauran. Sai Mu'awiyya bn Ammar (yana daga cikin sahabban Imam Sadik) ya tambayi Imam Sadik (a.s.) kan wannan matsala, sai ya ce da shi: "Ka soma da hajjin domin hajji farilla ne, sauran kuma a aikata nafilolin". Sai Abu Hanifa ya yi wannan ya yi wannan fatawar ya sauya ra'ayinsa([251])". Abu Kasim Al-Baggar ya kawo cikin Musnad na Abu Hanifa, cewa Hasan bn Ziyad ya ce: Na ji Abu Hanifa yana ba da amsar wannan tambayar: Wane ne mafi sani cikin wadanda ka gani? Sai ya ce: Ja'afar bn Muhammad. Yayin da al-Mansur ya kawo shi sai ya kira ni, ya ce: Ya Abu Hanifa, mutane sun fitinu da Ja'afar bn Muhammad, saboda haka ka shirya masa tambayoyi masu tsanani. Sai na shirya masa tambayoyi guda arba'in. Daga nan sai ya kira ni alhali kuwa a lokacin yana Hira ta kasar Iraki, sai na amsa masa wannan kira tasa na isa wajensa a lokacin kuwa Ja'afar bn Muhammad yana zaune a damansa. Yayin da na kalli Ja'afar, sai kwarjininsa ya shige ni, tamkar wannan kwarjinin bai shiga Mansur ba. Sai na yi masa sallama, ya amsa mini, sai na zauna. Sai Mansur ya ce: Ya Aba Abdillah, wannan Abu Hanifa ne, sai ya ce: "E, na san shi", sannan sai ya juya gare ni ya ce: "Ya Aba Hanifa, jefa tambayoyinka ga Abu Abdullah". Sai na rika jefa masa tambaya yana amsa mini, yana cewa: "Ku kuna cewa kaza, mutanen Madina suna cewa kaza, mu kuma muna cewa kaza. Ta yiyu mu dace da ku, ta yiwu kuma mu dace da su, wani lokaci kuma mu saba duka. Haka aka yi sai da na gama tambayoyin nan arba'in. Babu abin da ya gaza daga ciki. Sannan Abu Hanifa ya ce; "Lalle mafi sani cikin mutane shi ne wanda ya fi su sanin sassabawarsu([252])". Wadannan abubuwa biyu da suka faru a tarihi suna nuna yadda ake muhawara ta ilmi bisa tafarki mai tsari, yadda ake bijiro da mas'aloli da binciken hakika da gudanar da muhawara da fito da amsa. Irin yadda Abu Hanifa ya yi muhawara da Imam Sadik (a.s.) da tafarkin da suka bi wanda Musulunci ya tabbatar shi ya cancanta malamai da masu bincike su bi domin hakan Musulunci ya sanya ya zama ginshikin isa zuwa ga hakikanin gaskiya. Muna iya ganin misalin bin wannan hanya ta ilmi da tunani kubutacce a guri Shaikh al-Azhar, Shaikh Mahmud Shaltut yayin da ya fitar da fatawa cewa ya halalta wa musulmi masu bin mazhabobin Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya da Hambaliya, su bi mazhabar Shi'a Imamiyya kamar yadda ya halalta a bi sauran mazhabobin Musulunci, kuma aikinsu ingantacce ne karbabbe. Baya ga haka kuma Dokta Muhammad Muha-mmad Fahham, daya daga cikin Shehunan Azhar din shi ma yayi amanna da wannan fatawar.
|