Ahlul Baiti



"...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".

Inda ya ce: "Soyayyar ta Alayen Muhammadu (s.a.w.a) ce([76])".

Hadisan da suka zo game da so da kaunar Ahlulbaiti (a.s) da kuma yin musu da'a da lizimtarsu, ba za su kirgu ba cikin wannan dan karamin littafi, sai dai mun zabi sashi ne daga cikinsu kawai, don kuwa kowanne daya daga cikinsu (Ahlulbaiti) (a.s.) rana ce mai haske a cikin littattafan hadisi da ruwayoyi.

To amma domin a kara arzurta mai karatu da kara karfafa abin da zai kara masa sanin Ahlulbaiti (a.s) da kuma karfafa dangantaka da su, da mai da shi mai ta'allaka da su, mai rayuwa bisa tafarkinsu, don ya samu nasarar samun cetonsu, bari mu sake ambaton wasu daga cikin hadisan da suka zo game da su:

(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin al-Awsad daga ibn Hajar (r.a.) cewa; "Karshen abin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya furta shi ne: "Ku wakilce ni cikin Ahlulbaitina([77])").

(Dabarani ya fitar da hadisi cikin littafin Al-Awsad daga Jabir bn Abdullah (r.a.) ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba, na ji yana cewa:

"Ya ku mutane! (Duk) wanda ya fusata mu, mu Ahlulbaiti, Allah Zai tashe shi ranar kiyama yana bayahude([78])".

(Muslim da Tirmizi da Nasa'i duka sun ruwaito daga Zaid bn Arkam cewa, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ina tunatar da ku Allah game da Ahlulbaitina([79])".

Alkhatib ya fitar a cikin littafin Tarihinsa daga Aliyu (r.a.) cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Cetona ga al'ummata, na ga wanda ya so Ahlulbaitina([80])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next