Ahlul Baiti"Kuma abin da kuka saba wa juna a cikinsa, ko mene ne, to hukumcinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah". Alkur'ani yana hana mu mayar da jayayya ta ilimi da shar'antawa zuwa wata matsala ta rarraba da sabani da gaba da keta al'ummar musulmi, ya ce: "Kuma kada ku yi jayayya har ku raunan, karfinku ya kau....". (b). Mas'alolin da suke da alaka da siyasa ko zamantakewa wadanda shugaban al'umma, na shari'a, shi yake tsara su da gudanar da su, to wajibi ne a yi masa biyayya domin kada ra'ayoyi su yawaita a sassaba. Domin dole ne al'ummar musulmi ta zama tana da matsaya guda kan sha'anin siyasa da zamantakewar al'umma. "...Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzon Allah da ma'abuta al'amari daga cikinku". Hakan kuwa matukar su ma'abuta al'amari sun lizimci hukumce-hukumcen shari'a, kuma suna tabbatar da maslahar al'umma. Musulmi a yau - alhamdu lillahi - suna tare da Littafin Allah, wanda barna ba ta shigo masa ko a farko ko a karshe, duk wani mai jirkitarwa bai iso shi, yana nan kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kawo shi: "Hakika Mu ne Muka saukar da ambato (Alkur'ani), kuma hakika Mu masu kiyayewa ne a gare shi". (Surar Hijiri, 15: 9) Na biyu kuma, Musulmi sun hadu kan kubutar Alkur'ani daga dukkan wani ragi ko kari, kana kuma sun yi imani da shi da kuma Wanda Ya saukar da shi,
|