Ahlul Baiti



(إنَّما يُريدُ الله لِيُذْهِبَ عنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَيْتِ ويُطهِّرَكُمْ تَطْهيراً )

"...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa([74])". (Surar Ahzabi, 33:33)

5- Hadisin Soyayya:

Mun riga da mun yi magana kan Hadisin Soyayya wajen tafsirin Ayar Soyayya, kuma mun ambaci wasu masu ruwaya da suka ruwaito shi da kuma daga wajen wadanda suka ruwaito shi. A nan za mu sake ambaton hadisin ta hanyoyin daban ne, kuma zai kasance mai amfani mu ambaci sashin abin da ya taho daga Annabi (s.a.w.a) a kan son Ahlulbaiti (a.s) da kaunarsu a wasu ruwayoyin na daban.

(Imam Ahmad da Dabarani duk sun ruwaito daga Ibn Abbas (r.a.) ya ce: "Yayin da Ayar Soyayya, wato "Ka ce: "Bana tambayarku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta", ta sauka, sai mutane suka ce: Ya Manzon Allah, su wane ne makusanta wadanda soyay-yarsu ta wajaba a kanmu?, sai yace:

"Aliyu da Fadima da 'ya'yansu guda biyu".

Al-Bazzaz da Dabarani sun ruwaito cewa Hasan dan Aliyu (a.s.) yayi huduba wata rana yana cewa: "Wanda ya sanni to ya sanni, wanda kuwa bai sanni ba, to ni ne Hasan dan Muhammadu (s.a.w.a). Ni ne dan Mai albishir, ni ne dan Mai gargadi, ni ne dan mutanen gida wadanda Allah Ya farlanta son su a kan kowane musulmi, Ya kuma saukar a kansu (da ayar), "Ka ce: Ba ni tambayar ku wani lada a kansa face dai soyayya ga makusanta. Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau,
Za mu kara masa kyau a cikinsa". To aikata kyawawan shi ne soyayyarmu, Ahlulbaiti([75])".

Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa:

"...wanda ya aikata wani abu mai kyau, Za mu kara masa kyau a cikinsa".

Al-Saddi ya ruwaito daga Abi Malik daga ibn Abbas (r.a.) dangane da fadin Allah Madaukaki cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next