Ahlul Baiti"Haka Alkur'ani ya ci gaba a kan wannan gagarumin tafarki daga wannan al'umma zuwa wancan, kana iya ganin duban dubata na littattafa da mahaddatansa, kuma haka aka ci gaba da buga wasu Kur'anan daga wasu, wasu daga cikin musulmi suna ji da karanta shi daga wasunsu……ko da yake muna cewa dubbai ne kawai, amma fa daruruwan dubbai ne ko ma a ce dubban dubbai. Babu shakka, babu wani al'amari na tarihi da ya sami irin wannan inganci da wanzuwa wacce take a sarari tamkar abin da Alkur'ani ya samu, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawari cikin Surar Hijr: "Lalle Mu ne Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika, Masu kiyayewa ne a gare shi". Da kuma fadinSa Ta'ala cikin Surar Kiyamati: "Lalle ne wajibi ne a gare Mu, Mu tara shi, Mu (tsare maka) karatunsa". To idan ka ji wani abu kan jirkitar Alkur'ani da bacewar sashensa, daga bakaken ruwayoyi, kada ka ko kula su sannan ka fadi duk abin da ilmi yake yarda da fadinsa na daga sassabawar su da rauninsu da raunin masu ruwaitosu da sabawarsu wa musulmi, da kuma raunin da abin ruwaitowarsu - rusashshe - ya zo da shi([93])". Shehin malamin ya ci gaba da cewa cikin tafsirinsa karkashin fasalin: "Maganar Imamiyya Kan Cewa Babu Tawaya Cikin Alkur'ani", inda yace: "Ba a boye yake ba cewa Shaihin masu hadisi wanda aka san shi da kula da abin da yake ruwaitowa, wato Shaikh Saduk (Allah Ya kyautata makwancinsa) ya fada cikin littafinsa al-I'itikad cewa: "Akidarmu ita ce cewa Alkur'anin nan da Allah Ya saukar wa AnnabinSa (s.a.w.a) shi ne dai wanda yake cikin bangwayen nan biyu (wanda kowa ya sani) bai kuma wuce haka ba, wanda kuwa ya danganta mana cewa mun ce ya fi haka, to shi makaryaci ne". Shaikh al-Mufid a littafinsa na al-Makalat ya kawo cewa wasu jama'a daga cikin Imamiyya sun ce shi Alkur'ani ba a tauye ko da kalma ko aya ko sura daga cikinsa ba, amma an shafe abin da yake tabbatacce cikin Mus'hafin Amirul Muminina (a.s) na tawili da tafsirin ma'anoninsa bisa hakikanin saukarwa. A cikin littafin Kashful Gida'i fi Kitabil Kur'an, a fasali na takwas, kan tawayar Alkur'ani an ce: Babu shakka cewa an kiyaye shi daga tawaya da kiyayewar Sarki Mai sakamako, kamar yadda Alkur'ani ya yi nuni da hakan a sarari, kuma malamai suka hadu a kai. Shaikh Baha'i yana cewa: "Kuma haka nan an yi sabani kan aukuwar kari da tawaya cikinsa, abin da ya inganta shi ne shi Alkur'ani mai girma kiyayayye ne daga hakan, kari yake ko ragi, kuma lalle fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "Kuma lalle Mu, hakika Masu kiyayewa ne gare shi" yana nuni da kuma tabbatar da hakan. Al-Mukaddas al-Bagdadi cikin Sharhin al-Wafiya yana cewa:
|