Ahlul Baiti[14] Tabataba'i daga Sheik Tusi. [15] Wannan tawaga ta kumshi manya-manyan shuwagabannin kiristocin Larabawa kamar haka: Abdul Masih, wanda ya kasance shugabansu, da kuma al-Ayhma, wanda ya kasance mai kula da al'amurran gudanarwa da ayyukan ibada, da kuma Abu Hatam ibn Alkama, wanda ya kasance bishof ne kana kuma kula da makarantunsu. Dubi Fusul al-Muhimma na Ibn Sabbag al-Maliki a sashin gabatarwar marubuci. [16] Yin 'yar kure tsakanin vangare biyu kan Allah Ya saukar da azaba a kan vangaren da ba ya kan gaskiya. A takaice dai yin la'ananneniya tsakanin vangarori biyu don gano wani vangare ne ya ke kan gaskiya. [17] Ashabul Kisa' (ma'abuta mayafi), suna ne da ake kiran mutanen da suka kasance tare da Manzon Allah (s.a.w.a.) cikin mayafinsa inda daga baya aka saukar da Ayar Tsarkakewa a gare su. Su ne kuwa: Aliyu, Fadima, Hasan da Husaini (a.s.), kamar yadda aka ambata a baya. [18] Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi. [19] Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a kan Ayar Mubahala. [20] Jumlar "....ku yi salati a gare shi.." wacce ta zo cikin ayar tana nuni da wajibci ne, don malaman Usul al-Fikh sun bayyana fi'ilin umurni a matsayin yana nuni ga wajibci ne, wasu ma suna ganin cewa a duk lokacin da fi'ilin umurni ya zo cikin Alkur'ani ko hadisi yana nuni ga wajibci ne sai dai idan akwai wani abin da yake nuni da cewa wajibcin ya koma zuwa ga mustahabi. [21] Tafsirul Kabir na Fakhrurrazi a tafsirin Surar Ahzab aya ta 56. [22] Almizan fi Tafsiril Kur'an na Allamah Tabataba'i, juzu'i na 16, shafi na 344. [23] Allamah Hilli wanda ya kasance daga cikin manyan malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s), kuma yana daga cikin sanannun karni na bakwai bayan hijira, yayin da yake ambaton wajiban salla yana cewa: (Na bakwai) tahiya, wajaba ce a dukkan salla mai raka'o'i biyu sau guda, sannan kuma sau biyu a salloli masu raka'o'i uku da hudu, da mutum zai bar ta da gangan, to salla ta vaci. Akwai abubuwa guda biyar a cikin ko wane daya daga cikinsu da suka kasance wajibai, su ne kuwa: zama gwargwadon tahiya, yin shahadojin nan guda biyu da salati ga Annabi da Alayensa (a.s.). Dubi Shara'ii Islam, juzu'i na 1, babin salla.
|