Ahlul BaitiA cikin littafin Sharh al-Aka'id na Shaikh Mufid an ce: "An ruwaito daga Abul Hasan na Uku (a.s.) yayin da aka tambaye shi batun ayyukan bayi; shin halittattu ne daga Allah Ta'ala? Sai ya amsa da cewa: "Da Shi Ya halitta su da bai barranta da su ba, alhali Yana cewa: 'Lalle ne Allah Barrantacce ne daga masu shirka'. Barrantan nan ba ta shafar zatinsu, Ya dai barranta ne daga shirkarsu da munanan ayyukansu([183])". A cikin littafin Kitabul Tauhid na Muhammad bn Ajlan, ya ce: "Na tambayi Abu Abdullah (a.s.) cewa: 'Shin Allah Ya sakar wa bayi al'amarinsu ne?', sai ya ce: "Karimcin Allah ya wuce gaban Ya saki al'amurransu gare su", sai nace: 'To kenan Allah Ya tilasta wa bayi aikata ayyukansu kenan?, sai ya ce: "Adalcin Allah Ya wuce gaban tilastawa bawa yin wani aiki sannan kuma Ya azabta shi a kan wannan aiki([184])". A ruwaito cikin Uyunul Akhbar al-Ridha (a.s.) wajen fadar Allah Ta'ala cewa: "Kuma Ya (Allah) bar su a cikin duffai, ba su gani". (Surar Bakara, 2: 17) Abu Abdullah (a.s.) ya ce: "Ba a siffanta Allah da bari kamar yadda ake siffanta halittunSa, sai dai yayin da Ya san cewa ba su dawowa ga barin kafirci da bata ba, sai Ya hana su taimako da ludufi (tausayi), Ya bar su da zabinsu([185])". Har ila yau ya zo cikin wannan littafin wajen tafsirin Imam Ridha (a.s.) kan fadin Allah (S.W.T.) cewa: "Allah Ya sa rufi a kan zukatansu".
|