Ahlul Baiti



Sai ya ce: "Ya shugabana, ya ya zan zauna alhalin kana tsaye?! Yayin da Ali bn Ja'afar ya dawo gurin zamansa sai abokansa suka dora sukarsa, suna cewa: 'Kai baffan babansa ne kuma ka ke yi masa haka!!

Sai ya ce: "Ku saurara - sai ya kama gemunsa - idan Allah Mai girma da Daukaka bai nufi wannan furfurar da cancantar shugabanci ba amma Ya nufi wannan saurayin, Ya kuma ajiye shi inda Ya ajiye shi, shin zan yi inkarin falalarsa ne? Muna neman tsarin Allah daga abin da kuke fadi, kai bari dai ni bawansa ne ma([154])!".

Mahmud bn Wuhaib al-Bagdadi al-Hanafi ya ce:

"Muhammad al-Jawad bn Ali al-Ridha, sunan kunyarsa shi ne Abu Ja'afar", daga nan sai ya ce: "shi ne magajin babansa wajen ilmi da fifiko, ya fi duk 'yan'uwansa daraja da kamala([155])".

10- Imam Aliyu bn Muhammad al-Hadi (a.s.):

Amma Imam Ali al-Hadi (a.s.) dan Imam Muhammad al-Jawad (a.s.) lallai yana da falala mai girma da daukakar al'amari wajen ilmi da tsantsaini, tamkar abin da Mahaifansa masu kyauta suke da shi. Ana masa alkunya da Abul Hasan.

Mu'min al-Shabalanji ya ce:

"Ya kasance mai yawan munajati (addu'a), an fadi cikin al-Sawa'ik cewa: Abul Hasan ya kasance magajin babansa wajen ilmi da kyautattaki([156])".

Abdulhayy bn al-Ammad al-Hambali ya ce:

"Abul Hasan, Ali bn Muhammad bn Ali al-Ridha bn al-Kazim, Musa bn Ja'afar al-Sadik, ba'alawiyye, bahusainiyye, wanda aka fi sani al-Hadi, ya kasance fakihi ne kuma shugaba mai yawan ibada([157])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next