Ahlul Baiti



Don dada tabbatarwa, bari mu kawo dukkan wadannan fatawoyi don amfaninmu gaba daya:

Fatawar mai girma Shaikhul Azhar kan halalcin aiki da Mazhbar Shi'a Ithna Ashariyya:

An tambaye shi cewa: "Wasu mutane suna ganin wajibi ne kan musulmi ya yi taklidi (koyi) da mazhabobin nan guda hudu sanannu, kuma babu mazhabar Shi'a Imamiyya ko Shi'a Zaidiyya a cikinsu, domin aikinsa na ibada da mu'amala ya zama ingantacce, karbabbe. Shin Malam yana muwafaka da wannan ra'ayi, misali yana hana aiki da mazhabar Shi'a Imamiyya, ga misali?"

Sai Mai girma ya amsa da cewa:

1.  Lalle addinin Musulunci ba ya wajabtawa wani daga mabiyansa da ya bi wata mazhaba kebabbiya. Kai kowani musulmi yana da hakkin, tun daga farko, na ya bi kowace mazhaba wacce aka nakalto ta nakaltowa sahihiya wacce aka rubuta hukumce-hukumcenta cikin littattafanta kebantattu. Kuma duk wanda yake bin wata mazhaba daga wadannan mazhabobi yana da damar ya koma wata mazhabar, kowace ce kuwa. Kuma ba shi da laifi kan kome daga wannan.

2.  Lalle mazhabar Ja'afariyya wacce aka fi sani da Mazhabar Shi'a Imamiyya Ithna Ashariyya, mazhaba ce wacce ta halalta a yi ibada da ita bisa shari'a kamar sauran mazhabobin Ahlussunna. Ya kamata musulmi su san wannan, kuma su kubuta daga 'yan garanci wajen son wata mazhaba ayyananna. Addinin Allah da shari'ar-Sa (S.W.T.) ba su takaita da wata mazhaba ba. Duk (ma'abuta mazhabobin) ma'abuta ijtihadi ne karbabbu wajen Allah Ta'ala, ya halalta ga wanda bai cancanci bincike da ijtihadi ba ya yi taklidi da su da aiki da abin da suka tabbatar da shi cikin fikihunsu. Kuma babu bambanci tsakanin ibada da mu'amala a wannan".

(Mahmud Shaltut)


Maganar Dr. Muhammad Muhammad Fahham,
Shehin Jami'ar Azhar dangane da fatatar Shaik Shaltut:

"Allah Ya jikan Shaikh Shaltut wanda ya waiwaici wannan ma'ana mai girma ya dawwamar da ita cikin fatawarsa mabayyaniya mai gwarzantaka, yayin da ya yi furuci da halalcin aiki da mazhabar Shi'a Imamiyya yana mai daukar ta a matsayin mazhabar fikihu a Musulunci, mai dogara kan Littafin Allah da Sunna da dalili. Allah na ke roko Ya ba da dacewa wa masu aiki bisa wannan tafarki mai girma na gane juna cikin 'yan'uwa masu bin akidar gaskiya ta Musulunci".

"Kuma ka ce: Ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai".

Kuma karshen kiranmu Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next