Ahlul BaitiDaga cikin abin da ya rubuta wa manyan mutanen garin Basra kuwa, cewa ya yi: "Ni ina kiranku zuwa ga Littafin Allah da Sunnar AnnabiSa (s.a.w.a), domin an riga an kashe sunna an raya bidi'a. To idan kun saurari fadina kuka bi umurnina zan shiryar da ku tafarkin shiriya. Aminci ya tabbata a gare ku da rahamar Allah ([231])". Hakan nan Imam Husaini (a.s.) ya tabbatar wa al'umma yadda shari'a ta yi umarni da sabawa azzalumin shugaba, ya kuma yi shelar rukunan jihadi mai tsarki, domin sauya hukumcin azzalumai. Bayan jihadin Imam Husaini (a.s.) mai albarka, Ahlulbaiti (a.s) sun taimaka wa yunkuri daban-daban da Alawiyyawa suka yi tsawon sama da karni biyu, a fadin kasashen musulmi. Zaid bn Ali bn Husaini, wato dan Imam Zainul Abidin kuma jikan Imam Husaini (a.s.) ya yi yunkuri a shekara ta 121 bayan hijira. Wannan kuwa ya faru ne a zamanin Imam Sadik (a.s.) wanda kuwa ya goyi bayansa ya kuma yi juyayin shahadar Zaid(*). Fudhail Rassan ya ce: "Na shigo wajen Abu Abdullah (a.s.) bayan an kashe Zaid bn Ali, sai aka shigar da ni cikin uwar daki, sai ya ce da ni: "Ya kai Fudhail, an kashe baffana? Sai na ce 'fansar ka nake (e an yi haka), sai ya ce:"Allah Ya jikansa, lallai shi ya kasance mumini mai sani, mai ilmi, mai yawan gaskiya. Lallai da ya yi nasara da ya cika alkawari. Lallai da ya sami mulki da ya san inda zai sanya shi ([232])". Haka aka yi ta samun taimakawar Ahlulbaiti (a.s) wa masu yunkurin kawo gyara cikin Alawiyyawa. Daya daga cikin bayyanannen misalin irin wannan mataki na siyasa kuwa, shi ne matakin da Imam Kazim (a.s.) ya nuna dangane da yunkurin da Husaini bn Ali ya yi a shekara ta 169 a birnin Madina, yunkurin da aka fi sani da Yunkurin Fakh ([233])(*) wanda aka yi shi a watan Zulkida na wannan shekarar. Duk da cewa Imam Kazim (a.s.) ya ga alamun rashin nasarar yunkurin a wancan lokacin, babu shakka magan-ganun da ya yi sun nuna cewa yana goyon bayan ra'ayin jihadi. Ga abin da ya fadi wa shi Husainin yayin da ya ga yayi niyyar fita wannan arangama:
|