Ahlul BaitiDon haka, aikin Manzo (s.a.w.a.) yana bukatar tafsiri domin mu gane wajibi da mustahabi da kuma ja'izi. Malamai wadanda suka kebanta da wannan fannin suna rarrabewa cikin fahimta da tafsirin 'aiki' a cikin Sunna, ta hanyar hujjoji da alamomi da tafarkin bincike na ilmin Usulu. 3. Yarda (Takriri): Shi ne yin shirun Manzo (s.a.w.a) kan wani aikin da sahabbansa suka aikata, ya gani kuma bai hana su ba, kamar mu'amalolin zamantakewa da aikin mutum shi kadansa. To hakan ikirari ne da kuma yarda daga wajen Manzon Allah (s.a.w.a.), yana kuma shiga karkashin Sunna. To kamar haka ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta iyakance yadda ake mu'amala da Sunna mai tsarki da tafarkin tabbatar da ingancinta da tafsirinta. Tafarkin Bincike da Tabbatarwa: Malaman mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suna da hanyar bincike da tabbatar da Sunnar Annabi (s.a.w.a) wacce Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka iyakance kuma suka bayyana tushenta da alamominta. Mun riga mun yi nuni ya zuwa ga ruwayoyin da suka zo kan hakan a baya. Bisa wannan tushen malaman fikhun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka kafa tafarkin gyara (nakdi) cikin aikin bincike na ilmi. Babu wata sunna da suke mika wuya wajen ingancinta tun farko, sai dai su dauki matakin shakka kan ingancin sunnar, sannan su ci gaba da kokkofi da binciken ruwayar da tabbatar da ingancinta, idan har ingancinta ya tabbata sai su yi riko da ita da kuma daukanta a matsayin hujja da kuma fitar da hukumce-hukumce daga cikinta. Idan kuwa rashin Bisa ga wannan bayani, malaman mazhabar Ahlul-baiti (a.s) ba su yi ikrari da samuwar wasu littattafan hadisai masu inganci, sake ba tare da wani kaidi ba. Sai dai kowane littafi dole ya rusuna wa bincike da gwaji kafin a tabbatar da ingancinsa. Misalin littattafai mashahurai a ruwaya wadanda suka tattara abin da ya taho ta hanyar Ahlulbaiti (a.s) su ne: 1. Al-Kafi na Shaikh Kulayni. 2. Al-Istibsar na Shaikh Dusi.
|