Ahlul BaitiAhlul Baiti
(Zuriyar Manzon Allah)
Mukaminsu Halinsu Da Tafarkinsu
Gabatarwar Mu'assasa
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:
"Ni mai bari muku nauyaya biyu ne tare da ku, littafin Allah da dangina, mutanen gidana (ahlulbaiti) wadanda in kun yi riko da su ba za ku taba bata ba a bayana har abada, kuma lalle ne su biyun ba za su rabu da juna ba har su riske ni a bakin tafki". Ahlulbaiti (a.s) makaranta ce mai haske kuma taurari ne a sararin samaniyar addinin Musulunci madaukaki. Su ne ja-goranci cikakke mai koyi da Manzon Allah (s.a.w.a.), sun sha daga ilminsa a gidansa suka tashi, sannan suka rayu bisa tafarkinsa. Suna masu kira zuwa ga Littafin Allah da kuma riko da sunnar AnnabinSa (s.a.w.a). Suna nuna misalai madaukaka ta hanyar halayensu, suna kira zuwa ga gaskiya, ba sa karkace mata ko da kamar dan yatsa. Kamar yadda hadisin Manzon tsira ya bayyana mana su (Ahlulbaiti) tagwaye ne na Alkur'ani mai girma, ba sa rabuwa domin su ne hakikanin tamka na Alkur'ani da duk abin da yake tattare da shi na ilminsa da tarbiyyarsa. Domin haka Alkur'ani ya ambace su a sarari: ( إنَّما ÙŠÙريد٠الله Ù„ÙÙŠÙذْهÙبَ عنْكÙم٠الرّÙجْسَ أهْلَ البَيْت٠ويÙطهّÙرَكÙمْ تَطْهيراً ) "...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen Babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33) Domin yawan ayoyin da suka sauka game da Ahlulbaiti (a.s) da kuma hadisai bayyanannu wadanda aka yi furuci da su, lallai Ahlulbaiti (a.s) sun zama abin kauna ga zukatan musulmi na kasashe da zamunna daban-daban, suna kwarara zuwa gare su domin su sha daga tabkin ilminsu kuma su nemi karuwa daga hasken masaniyyarsu. Duk wanda ya kyautata karatun tarihin Ahlulbaiti (a.s) da aikin da suka yi na ilmi, zai san rawar da suka taka, wacce ita ce ta kan gaba, zai kuma san aiki mai girma da suka yi. Lallai sun yi matukar dagewa wajen kiyaye tsarkakar shari'a da kuma tsare asalin akidar Musulunci har ma suka sadaukar da kansu da yin jihadi domin tabbatar da ka'idojin nan madaukaka a aikace da ja-gorancin al'umma bisa shiriyar wadannan ka'idojin. A kullum tarihin Ahlulbaiti (a.s) madaukaka yana bayyana a matsayin rayayyiyar baiwa wadda take da tasiri ga tunanin al'umma da kiyayewarta, tana wadatar da rayuwarta tana kuma daukaka wayewarta. Babu shakka, Ahlulbaiti (a.s) su ne kudubin al'umma, su ne rumfa matattara mai hada kan al'umma don gyara. A cikin wannan matakaicin littafin, mun yi kokarin bayyana sashin abubuwan da rayuwar Ahlulbaiti (a.s) ya kunsa da kuma abin da ya ta'allaka da martabarsu da rawar da suka taka a tarihi. Game da gabatar da wannan littafin, muna kwadaitar da 'yan'uwa musulmi da su samu fa'idantuwa da shiryarwa ta Ahlulbaiti (a.s) da aiki da ita da komawa wajen wannan ja-gaban da kuma koyi da shi da tsayawa sahu guda don fuskantar 'yan rahoton nan masu kokarin raba kan musulmi da wargaza hadin kansu, a dai-dai lokacin da al'ummarmu ta Musulunci take shiga gumurzu mai tsanani tsakaninta da 'yan mulkin mallaka da 'yan gurguzu da yahudawan sahayoniyya, wannan gumurzun kuwa sakamako ne na tabbatar da sakon Musulunci da kuma (kokarin) rayuwa karkashin inuwar adalcin Ubangiji. Muna kuma kira ga al'ummar musulmi da su fuskantar da dukkan karfinsu wajen kira zuwa ga Musulunci da kare tsarkakan abubuwansa da tauye damar wadanda suka saba shuka sabani da watsa gubar banga-ranci tsakanin al'ummar musulmi. Ya ku al'ummar Annabi Muhammadu mai girma! Ya masoya Ahlulbaiti! Ya zama wajibi a gare ku da ku hada kai da kuma karfinku waje guda, domin kuwa wannan al'umma, al'umma ce guda, kuma daukakarku da kara-marku ba sa tabbata sai da riko da sakon Musulunci da kuma aiki da Littafin Allah da Sunnar AnnabinSa (s.a.w.a). "Kuma ka ce: ku yi aiki, sa'an nan Allah Zai ga aikinku da ManzonSa da kuma muminai". (Surar Tauba, 9:105)
|