Tarihin Fatima Zahra [a.s]A kasar idan kuwa ya zama ranar maulidin haihuwar Manzo ne, wannan ranar babu wata ranar buki a kasar wacce ta kai ta ko ta yi kusa da ita. Mutane gaba dayansu za su fito da manyan fitilu su jera su da filawowi da manya-manyan kayan kwalliya da na alatu su jera su a gefen titi har sai ya zamo kamar ba za ka iya bambance tsakanin dare da rana ba! mai bukata saboda murna da haihuwar Manzon Allah (SAAW). A wannan rana sai ka ga mutane suna zagayawa ko'inna suna murna suna yawaita salati don murna da zagayowar ranar da aka haifi Shugaban Manzanni da halittu baki daya. LITTAFAN DA MUKA YI AMFANI DA SU:
1. AL-MIL AL WA NAHAL Na Imam Zahabi (Sunni) 2. KASHAFUL GUMMA Na Allama Ardabily 3. BIHARUL ANWAR Na Allama Majalisi 4. ASHIFA Na Alkali Iyad 5. SIRAIBNISHAK Na Ibn Ishak 6. NURUL YAKIN Na Shaik Muhammad Al-khadari 7. FATIMA MINAL MAHADIILAL LAHADI Na Kaziwini
|