Tarihin Fatima Zahra [a.s]



In shauki ga Allah da lahira yake sa gudun duniya, ba sai na fada ba. mai karatu yana iya kirdadon zuhudunta. In hankali. ilimi da imani ake auna zuhudun mututn da shi ba sai an fada ba, mai karatu yana ganin cewa duk halitta baki daya babu mai zuhudunta, sai mahaifinta, mijinta ta da Annabi Isa (as). Wanda har ya koma zuwa sama bai taba mallakar shimfida ba barc gurin kwana. An taba yi mishi magana a kan cewa ba zai sayi doki ba saboda yawan tafiya a kasa? Sai ya ce kimar sa a wajen Allah ta wucc Allah ya bautar da shi da doki! Maana ba zai iya barin lokacinsa na lbada ba ya tafi nemowa doki abinci.

IBADAR NANA FATIMA (AS)

Nana Fatima (AS) kamar Mahaifinta take wajen ibada, tana mai godiya ga Ubangijinta a kan niimomin da ya yi mata, wadanda ba sa misaltuwa. Takan tsaya tana salla har kafafuwanta su kumbura! Wata rana Salmanul Farisi ya shigo masallaci ya ga Imam Aliyu ya yi sujuda ya daden gaske bai dago ba/sai ya ce lafiya? Ko da ya taba shi sai ya ji sam babu alamar rai tare da shi (ya yi fana'i) sai ya aiga wurin Fatima (as) hankalinsa a tashc! Da zuwa bayan ya yi sallama sai ya gaya mata Imam Aliyu ya rasu a masallaci yana sujuda. Sai ta fashe da dariya ta ce masa "Ya Salman mu Ahlul baitin Manzon AUah. duk sad da muka yi sujuda in muna salla mu kadai mukan yi fana'i ne mu bar wannan farfajiyar d.uniyar mu tafi fadar Ubangiji!

A shekara ta goma sha biyu bayan hijira, Manzo ya kirayi al'ummar musulmi baki daya zuwa ga aikin hajji, wanda daga ita Manzo bai kara yin wata ba (hajjul wada). Manzo ya nuna wa musulmi yadda aikin hajji yake. da hukunce-hukuncensa baki daya tun daga farko har zuwa karshe.

Bayan ana dawowa. an kai wani guri da ake kira Ghadir Khum sai ya yi umurni na gaba su tsaya. na baya kuma a jira su. Bayan al'ummar musulmi sun hadu ana tsananin zafin rana su wajen dubu sittin, sai Manzo ya ce a sanya masa mumbari zai lsar da sako ga dukkan musulmi baki daya, har ya ce wanda yake nan ya isar wa wanda ba ya nan. sannan naye su isarwa 'ya'yansu.

Bayan ya hau mumbarin ya yi huduba mai tsawo a kan shugabancin Imam Aliyu (AS) ga jama'ar musulmi da wajbicin mika masa wilaya da iyalan gidansa (Imamai) har inda yake cewa "Duk wanda ya san ni shugabansa ne, to Aliyu ma shugabansa ne. Ya Allah ka wulakanta wanda ya wulakanta shi. ka taimaki wanda ya taimake shi. har zuwa karshe.

Bayan ya gama sai jamaar musulmi suka dinga yi masa murna suna yi masa bai'a. har Umar Ibn Khaddab ya zo yana cewa: "Ya Aliyu ka wayi gari kana Shugabanu. ka miko hannu in yi maka bai'a.

Daga nan sai Manzo da sahabbai suka koma Madina. Bayan komawarsu Madina ba da dadewa ba sai zazzabi da rashm lafiya ya fara kama Manzo, har ta kai ga nuna alamar komawarsa ga Ubangijmsa. Yakan ziyarci makabartar musulmi na baki'a ya roka musu gafara wajen Ubangiji. Sannan kuma yana yi wa lyalan gidansa wasiyya a kan abubuwa da dama.

Nana Fatima (as) ta yi mafarki bayan hajjin bankwana ta ga tana karanta Kurani sai ya subuce ya bace. sai ta farka. Ko data bai wa Manzo laban sai yace "Nine wannan Kur'anin ya hasken idona. ba da jimawa ba za ki daina ganina."

Daga nan sai Manzo ya kwanta rashin lafiya. Kafm ciwon ya yi tsanani sai ya ta da rundunar yaki zuwa Rum, ya nada shugaban rundunar ya zama Usama bin Zaid. Sannan ya ambaci sunayen wasu daga cikin muhajirun ya.ce lallai su bi wannan rundunar, amma saboda wata manufa sai ba su bi rundunar ba.

Bayan nan sai rashin lafiyar ta yi tsanani har sai an ta da shi Nana takan kalle shi sai ta fashe da kuka ta zubar da hawaye mai yawan gaske. Wani lokaci kuma sai ta dube shi ta yi addu'a tanatunanin ko Allah (swt) zai ba shi lafiya, tana mai cewa: "Ya Ubangiijina ga Mahaifina gare ka, wanda babu wani Annabi wanda aka cutar wajen isar da sakonka kamar sa, ya dasa tutar Musulunci a ko'ina da ina a bayan kasa. Ni ma burina shi ne tutar Musulunci ta kafii a ko'ina a bayan kasa, duhun kafirci da zalunci ya gushe. Sai dai yanzu ya shiga wani hali na rashin lafiya. Ya Ubangijina ka ba shi lafiya, babu mai warkarwa sai kai."



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next