Tarihin Fatima Zahra [a.s]
Ko da Imam ya yi mata wannan bayanin. sai ta ce: "Ya Baban Hasan. kwana nawa ya rage min a tsakanin su. me ya fi kurkusa da su daina gani na gaba daya! Wallahi ba zan daina kokawan rabuwa da Mahaifma ba dare da rana har sai na riske shi!" Sai Imam Aliyu (as) ya ce: 'Ya 'yar Manzon Allah ki aikata duk abin da ya fi soy uwa a gare ki Daga nan sai Imam Aliyu (as) ya gina wa Nana (as) gida a wajen Madina a makabartan bakia ana kiran shi da suna Baitul- buka'i. Idan gari ya waye, sai ta kama hannun Hasan da Husaini (as) zuwa makabartan Baki'a, ta yi ta kuka cikin kabarurrukan musulmi. tana musu addu o i. In darc ya yi sai Imam Aliyu (as) ya zo ya dawo da su gida!
An ruwaito daga Mahamud Ibn Lubaid yana cewa: "Wata rana na zo zan wuce ta makabartan shahidan Uhudu. sai na ga Fatima (as) a wurin kabarin Sawadi Hamza (r.a) tana ta kuka tana mishi addu'a. Da zan fashe da kuka sai na jure har na iso gurinta. Bayan na mata sallama sai na ce: Ya Shugabata. zuciyata ta yi kusa ta fashe saboda wannan kuka naki." Sai ta ce: "Yaya kuwa ba zan yi kuka ba. alhali na rasa Mahaifina.mafi alkhairin Annabawa da mazanni sai na ce ya shugabata ina so in tambaye ki wata tambaya guda daya " Sai ta ce: "Ka yi tambayar da kake so." Sai na ce: "'Da gaske ne Manzo ya bawana wa al’ummar musulmi imamancin Aliyu (as) sadda yake raye?" Sai ta ce "Abin mamaki. ka mance ranar Gadir Khum ne'7' Sai na ce "Ban mance ba. Ina so in ji ko Manzo ya gaya miki ke da shi?" Sai ta ce "Wallahi na ji Manzo yana cewa: Aliyu khalifana ne bayana. Hasan. Husaini shugabanni ne Sannan shugabanni tara 'za su fito daga tsatson Husaini. duk wanda ya bi su ya tsira. wanda ya ki ya halaka. ya tabe.
AJALIN NANA FATIMA (as) YA CIKA !!!
Nana Fatima (as) ta yi kwana arbain tana kwance ba ta da lafiya. A daren kwana na arbain. sai ta yi mafarki da Mahaifinta ya gaya mata cewa washe gan za ta bar duniya ya zuw a gare shi. Da gan ya waye sai ta tashi ta daddogara ta debo kayan yaranta ta wanke. sannan ta yi musu wanka. hawaye na rubo mata. tana musu wankan bankwana! Mai karatu mu saurara a nan mu yi kukan wankewar karshe wanda Fatirna yar Manzon Allah (S.A W) ta yi kan Imam Husaini (as). kafin ta zo karbala ta ga yadda kafirai suka yaiika shi bayan ya yi shahada!!! Bayan ta gama sai ta konia kan shimfidarta ta kwanta. Daga nan sai ta kirawp Imam Aliy u (as) don ta yi mishi wasiyya.
WASIYYAR NANA FATIMA (as) GA IMAM ALIYU (as)
Lokacin da Nana (as) ta ga lallai lokaci ya karato. sai ta kira Imam Aliyu (as) don bawana masa abm da yakc cikin zuciyarta. Tana mai cewa "Ina ganin lokacin haduwata da Mahaifina ya yi nan ba da |imawa ba. saboda hakanakc so in yi makawasiyya." Sai Imam (as) ya ce: "Ƙi yi min y,asiwa da abin da kikc so ya diyar Manzon Allah' Sai ya fitar da duk wanda yakc gidan Sai ta ce: "Ya dan Ammina. ma fatan tun bayan haduwamui ba ka samc in mai karya ba, yaudara. ko saba maka ba Sai ya ce: "Ina neman tsari gurin Allah. Ƙin fi kowa sanin Allah. kin fi kowa nagarta. da tsoron Allah da kusanci. Hakika rabinya da ke ya yi min nauyin gaskc. Sai dai rabuwa ce wadda babu makawa Hakika kin dawo min da bakin cikin rabuwa da Manzon Allah (saw). Hakika rabuwa da ke da wafatinki ya nauyaya a kaina Inna lillahi wa mna. llaihir raji un! Sai suka fashe da kuka baki daya! Sai Imam ya dauki kanta ya jingina a kirjinsa. ya ce: "Ki yi min wasiyya da abin da kika so."Sai ta ce: "Ina maka wasiyya da ka aun Amamatu (diyar "yar uwarta Zainab) za ta kasance mai tausasawa ga yarana kamar ni. Sannan ta ce: kada ka bar wadanda suka zalunce ni su halarci jana'izata, kar waninsu yay 1 min salla daduk wadanda sukabi su. Karufe ni dadaddare sad da kowa ya yi barci!!!
"Ya dan Ammina! Idan na cika. ka yi min wanka tare da suturata domin ni tsarkakkiya ce abar tsarkakewa. Ka yi min wanka da ragowar magarya da kafiir din da aka yi wa Manzon Allah wanka da shi (wanda Malaika Jibrilu ya kawo mishi lokacin da zai yi wafati)"
Ga wata ruwayar kuwa: 'Ya dan Ammina. ina maka wasiyya da ka auri Amamatu. Ina maka wasiyya in ka yi aure ka sanya dare da yini ga matarka, sannan ka sanya dare da yini ga 'ya'yana. Kar ka bari su sami jin mahaifiyarsu ba ta nan cikin gidanka har maraici ya dame su. Ina maka wasiyya ka dauke ni a makara irin wacce Mala'ika Jibrilu ya nuna min " Sai Imam ya ce ta siffanta inn shi. sai ta siffanta. shi kuma ya nemoirinsa "InamakawasiyyadakabaiwakowaccedagamatanManzo kudi Ukiya goma sha biyu. Su ma matan Banu Hasim kowacce ka ba ta haka," Sannan ta ce a bai wa Amamatu wasu daga cikin kudin.
An ruwaito daga Ibn Abbas yana cewa: "A cikin wasiyyar da Nana Fatima (as) ta rubuta akwai inda take cewa: Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai. wannan shi ne wasiyyar Fatima 'yar Manzon Allah: Ta shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Annabi Muhanimad bawansa ne. Maiizonsa ne. Lallai Aljamiah gaskiya ne. wuta gaskna ne. tashin kiyama gaskiya ne. babu shakka cikinsa Lallai Allah zai tayar da wadanda suke cikin kabari.
Ya Aliyu: Ni ce Fatima binti Muhammad. Allah ya aurar maka da ni ne don in zama taka duniya da lahira. kai ka fi cancanta da ni fiye da waninka. ka yi min wanka ka sanya min likkafanina. ka yi min salla da daddare. ka bin ne ni a daren ba tare da wani ya sani ba. Na bama Allah amanar ka. sannan ina yi wa 'ya'yana sallama ta bankwana."
Rashin lafiyan Nana (as) ya yi tsanani har Imam Ali (AS). Asmauu. Hasan. Husaini. Zainab da Ummi Khulsum (as) ba su iya barin gurin daidai da sakon daya. Takan suma ta farfado. ta suma ta farfado. Duk lokacin da ta farfado idanuwanta suna kallon yayanta. kallo na tausayi da bankwana
Imam Aliyu (a,s) yana cewa " Daren da Allah (swt) ya yi nufi ya karrama ta ya dauke ta ya zuwa gare shi, takan amsa sallama, sai ta ce: "Ya dan Ammina Mala'ika Jibrilu ne ya zo yana min sallama yana cewa: "Allah mai Aminci yana gaishe ki, ya masoyiyar Masoyin Allah, fiiran zuciyarsa, yau za ki hadu da jama'a madaukakiya a Aljanna madaukakiya. Sannan sai ya juya ya tafi."
|