Tarihin Fatima Zahra [a.s]An ruwaito cikin Sunan Abi Dawud da nisa daga Aus Ibn Aus yana cewa: Manzon Allah (SAAW) yana cewa: Mafificin rana daga cikin ranekunku shi ne Juma a. saboda haka ku yawaita yi min salati a cikinsa. domin ana bijiro min da salatinku. Ya zo a cikin Attawassul na Shaikh Ja'afar Subhani yana cewa: Manzo yana cewa: Manzo ya ce: Allah (SWT) yana da Malaiku masu kewayawa koina a doron kasa. suna isar rrun da salatin alummata a gare ni. Manzo (SAAW) yana cewa: Babu wani mutum wanda zai yi min salati face Allah ya mayar mani da ruhina na mai da masa da sallama. "'Duk wanda ya yi min salati a kabanna zan ji shi. Wanda ya yi min daga nesa za a isar min." "'Ku yi min salati domin salatinku yana isowa gare ni daga duk 133 inda kuke. "Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina yji yi min sallama, zan mai da masa har sau goma. Kuma Mala'iku goma za su ziyarce shi suna masu sallama a gare shi." An ruwaito daga Amirul muminina Aliyu (AS) cikin Nahajul Balaga yana cewa: Idan kana da wat bukata gurin Allah ka fara da salatin Manzo, sannankaambaci bukatarka. Domin Allah mafi karimci ne akanatambaye shi abu biyu ya biya daya ya bar dayan. Wata rana na tambayi Malam Hamza Muhammad Lawal a kan yaya tasirin salati yake a kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran? Sai ya ce: kasar Iran kasa ce wacce take da yawan mutane a yanzu kamar miliyan 75. Kuma a duk lokacin da aka ambaci Sunan Muhammad (SAAW) babu wannda zai yi shiru face'ya yi masa salati, har kananan yara wadanda ba su yi girma sosai ba, saboda tarbiyyar da suka taso suka ga ana yi. Haka nan ma abin yake idan aka ambaci sunan wani Imami ko wani waliyyi daga cikin waliyyan Allah. "A kasar Iran babu wani taro wanda mutane za su tariu ko na shaanin addini ko bukukuwa, ko ziyara ko cin abinci face sun yawaita yi wa Manzo salati kafin su watse. wannan ana yin sa ne a matsayin hakkin zama ko taro. "A duk lokacin da Liman yake khuduba ko karatu cikin salla. ko wani mai wa'azi ya ambaci Muhammad (SAAW) to kaida ne ya tsaya har sai an yi wa Manzo salati kafin ya ci gaba.
|