Tarihin Fatima Zahra [a.s]Khususiyarki na da yawa da mijinki da "yan gidanki. Ayar da'am a kanki ta sauka da Ali mai gidanki. Ni ma miskini ne yatimun ne na zo gurinki. 7. Ni ma asirin ne na zo ni bara gun masu daula. 8. Duk duniyar ga ke ce da Baba Imamul Mursalina. Sannan ke kuma Sayyadatunisa'il alamina, Kuma ga Hasan, Husaini Sayyida Shababu janna. 9. Ko matan Mahaifinki sun san ta gabansu ke ce, In ko takama ne ke ai Hurul'ini ma ce. 10. Duk mulkin mace tana yin biki har da haila, Innama yuridullahu liyuzhiba ankum, in ji Allah. Liyuzhiba ankumrijisa ba dauda ko kalila. 11. Allah ya katange ta ba ta yin sabo Batula, Da ita da Maigidanta da 'ya'yaye nata duk jimilla. Maasumai ne gama ba sa yin sabo ko kalila, Zahara ina da sabo amma ke na rike wasila. 12 Dukkan mai isa da ta gan ki sai tai saranda*. Domin isarki aurenki ma an daura ne a fada. A can fada ta Allah ya ce ya ba Ali mai ibada. Allah da kansa yai walicci sai Manzonsa shaida. 13. Da ita Annabi kamar fatokofi in ka gan ta. Ta daidaita caf-caf babu tsayi kuma ba gajarta. Ta dauko Ma'aiki a gun maganarta da murmushinta. Da dukkan dabi’u har tafiyarta da waiwayenta
|