Tarihin Fatima Zahra [a.s]3. Fitintunu da bala Yi da al'ummar musulmi za su dinga shiga. sakamakon barin Imamancin Imam Aliyu (as) da sabawa wasiyyar Manzo. ta yadda shugabancin musulmi za* koma haiinun jabbirai mashaya giya da sunan khalifancin Mahaifinta!! Misali a rfan shi ney Kamar yadda ya zo cikin littafin Jalaluddeen Suyudi. Tankul - Khulafau, YAZID IBN MU'AWIWA (L) Waqid ya ruwaito daga Abdullahi Ibn Hamzala Gasil yana cewa: "Wallahi kafin mu fito don mu yaki Yazid Ibn Muawiwa (L) sai da muka yi zaton Allah ya yi kusa ya yi ruwan duwatsu na azaba daga sama saboda sabo; ya kasance inutun ne wanda yake aurcn yan mata tare da uwaycnsu. da kanncnsu mata.(yakan hada uwa. ya da kanwa daki guda a matsayin matansa). Mashayin giya ne sannan ga tozarta salla!" (shafil95) WALID IBN ABDULMALIK (L) Abu Nu'aim ya aiwaito ... yana cewa: Umar Ibn Abdul'aziz yana cewa: Walid ya kasance a Sham. Hajjaj a Iraki. Usman Ibn Hibbara a Hijaz da Karratu lbn Shank a Misra:- Zalunci ya cike ko'ina da ma a doron kasa!" (shafi 208) WALID IBN YAZID IBN ABDULMALIK Ya kasance fasiki. mashayin giya. me keta alfarmar addini. Ya yi nufin ya je aikin hajji. daga nan ya hau kan saman dakin Ka'aba ya sha giya! Sai mutane suka ki yarda. suka kama shi suka kashe shi. Lokacin da suka kama shi. sai ya ce " Ashe ban kyautata muka ba'.' Ban farfado da tattalin arzikin kasa ba?' Sai suka ce ba don kawunanmu za mu kashe ka ba, a a sai don keta alfamar addini, shan giya, auren matan babanka. ' Lokacin da aka kashe shi aka gutsire kansa Yazid Nakis ya dauki kansa ya soke a jikin mashi. Da dan uwansa Sulaiman Ibn Yazid ya dubi kan, sai ya ce: Allah wadaranka. hakika ya neme ni da luwadi amma na ki !!!' Ire-Iren wadannan Khalifofin na Musulunci sun fi tamanin a cikin sherkaru 800 zuwa dubu bayan wafatin Manzon Allah (S.A.W). Kuma saboda rashin bin wannan wasiyyar ta Manzo shi ya sa musulmin duniya suka rasa jagoranci guda wanda za su bi ya ba su kariya daga makiya. Mai karatu yana iya ganin abin da da ke faruwa da musulmi a sassa na duniya daban daban kamar:- Khashmir, Bosniya. Checheniya, Aljeria, Sabiya, Lebanon. Palasdinu, dss. Wadannan abubuwan da muka ambata su suka hana Nana (as) ta runtsa idonta ta yi barci, dare da rana kullun tana cikin kuka da bakin ciki. Har sai da tsofaffin Madina wadanda siyasa ta hana su su fahinci ko me ya sa Nana Fatima irin wannan kukan. suka zo gun Imam Aliyu (as) kai karan Nana. wai ta dame su da kuka! Da rana kukanta yana hana su neman abinci. da daddare kuma yana hana su barci da iyalinsu. sai dai ta zabi ko ta yi kukan rabuwa da mahaifinta da rana ko da daddare!
|